adam-zango-ya-tsorarta-da-fati-washa-a-wajen-saitin-fim

Wai! Abun har da hawayeAshe Fati Washa masoroyaciya ce?, kalli yadda Adam Zango ya tsorartar da ita

Zango ya nemi ya tsorartar da ita yayin da hau saman doki domin domin aiwatar da aikin da ya kamata tayi cikin wata sabuwar fim da direkta Hassan Giggs ke shiryawa mai take "Sadauki".

FItacciyar jaruma mai tashe Fati Washa ta kasa boye tsoron ta yayin da abokin sana'ar ta jarumi Adam Zango ya bata tsoro a saitin shirya fim.

Zango ya nemi ya tsorartar da ita yayin da hau saman doki domin domin aiwatar da aikin da ya kamata tayi cikin wata sabuwar fim da direkta Hassan Giggs ke shiryawa mai take "Sadauki".

Cikin wasa da dariya jarumin yake bugun dokin da jaruma ta hau sukuwa amma lamarin dukar ya bata tsoro domin bata son dabbar ya firgata har ya tsere ya kwala ta a kasa.
Duk da cewa ta roke shi da ya daina, Adam Zango ya cigaba ganin yadda lamarin ke sanya masu aiki a saiti dariya.
Abun ya kai har inda ta nemi tayi kuka duk da nanatawar da ake ta mata na cewa babu abun da zai faru da ita domin dokin ba zai kufce ba balle ya firgita sanadiyar dukar da Zango keyi.
Sai dai daga ganin yadda saitin wannan sabuwar  fim da ake shiryawa ana iya ganin cewa jarumai da ma masu aikin saitin suna kaba-ka-lashe a wajen domin ana aiki ana hada da dan nishadi.


EmoticonEmoticon