NOBLE'S:AUREN FANSA!!! NA 04

AUREN FANSA!!! Na
04

Zuciyarsa har wani zafi take masa, kwanciya yayi kan gadonsa yana mai maida numfashi sama sama, meyasa Bilki bazata ta6a chanza halayenta ba? Yasani tun kafin suyi aure yake fama da iri iren halayenta na nuni da maita akan kud'i, sam bata gajiya da tambayarsa kud'i, ko lokacin auren su Goggo taso ta hana don sam tarbiyyar Bilki bata yi mata ba, batada kamun kai ga shegen yawo, sai dai a lokacin yadda yake tsananin sonta baijin zai iya hak'ura da ita, a haka yayi ta lalla6a Goggo har ta amince akayi auren. Gashi sam bai iya mata fad'a idan tayi masa laifi sannan bai iya hanata kud'i idan ta tambayesa ya rasa dalilin da yasa haka. So da yawa idan ta tambayesa sai yaji kamar kar ya bata amma sam sai ya kasa haka yayi ta rayuwa da ita tana cutarsa ba tare da ya ankara ba. Gashi da anyi abu ta iya kukan k'arya kuma nan da nan sai zuciyarsa ta karaya yaji yana tausayinta, a haka ta gano lagonsa abu kad'an zata sa masa kuka. Ajiyar zuciya ya saki tare da gyara kwanciya yanzu yasan mafita d'aya ce ya k'ara aure k'ila hakan zai sa ya gane banbancin zama da Bilkin, wata k'ila ma wadda zai aura batada halayen Bilki ya yarda ya amince zai k'ara auren, tashi yayi da niyyar shiryawa yaje ya sanar da Goggo ya shirya ko yau za'a iya d'aura masu aure, wayarsa ta fara ruri. Goggo ya gani a saman screen d'in wayar haka kawai gabansa sai da ya fad'i. A sanyaye ya d'auka gami da yin sallama, da sauri Goggo tace "Hamza kana ina yanzu?" Yace "Inagida Goggo, lafiya dai ko?" Tace "Babu lafiya Hamza, maza maza ka taho asibiti k'anwarka na nan na nak'uda, kuma ta kafe tak'i shiga d'akin haihuwar wai sai ka zo, kuma ga haihuwar tazo kar ta haihu a gaban d'aki Hamza, kayi sauri don Allah." A rud'e yace "Gani nan yanzu wace asibiti ce?" Tace "Alheri clinic kayi sauri." "To." Kawai yace ya fito da gudu daga d'akin, takalmansa ma daban daban yasa tsabar rud'u ga gabansa sai fad'uwa yakeyi. Haka dai ya daure ya figi mota ya fice da sauri, duk da asibitin batada nisa daga gidansa amma gani yake bazai isa da sauri ba. Cikin k'ank'anin lokaci Hamza ya iso Alheri clinic da gudu ya shiga ciki yana tambayar suna ina. Koda yaje hanashi shiga akayi sai da ya kira Goggo yace gashi nan sun hana shi shigowa. Da k'yar ta rok'esu suka barshi ya shigo. Yana shiga ya iske Amina sai faman nak'uda takeyi mai zafi tana kiran sunan Hamza tana kuka. Da sauri ya isa gareta tana ganinsa ta k'ara sautin kuka tana fad'in "Ya Hamza na gode da kazo, wata magana zan fad'a maka." Jikinsa yayi sanyi yace "Koma meye ay sai ki bari ki haihu tukunna..." "Ya Hamza bazaka gane ba bazan iya bari sai na haihu ba, amma don Allah ka tsaya ka saurareni!" Ta fad'a cikin muryar tsawa, tashi yayi ya fara safa da marwa idanunsa sun kad'a sunyi ja, yasan tatsunniyar gizo bata wuce ta k'ok'i, tabbas yasan maganar da ta saba fad'a masa yau ma ita d'in ce zata fad'a masa. Don haka sai yace "Ko meye zaki fad'a na riga na sani, don haka ki tashi a shiga dake d'akin kar ki haihu a nan." Duk'awa tayi tare da fasa wata irin giggitaciyar k'ara wadda bama Hamza ba har Goggo da malaman asibitin sai da suka rud'e, fad'i take "Bazan shiga ciki ba ya Hamza sai kayi min alk'awari na k'arshe." Da sauri ya kalleta "Haba Amina! Meyasa kin faye kafiya ne? Ba mun gama maganar nan tun tuni ba? Meyasa kike tado zancen kuma, ki bari ki haihu zamuyi magana." Girgiza kanta tayi tana hawaye "Kayya ya Hamza, don Allah kayi min alk'awarin kawai." Goggo ce ta sa baki tace "Hamza kasan zafin haihuwa, kawai kayi mata alk'awarin a shiga da ita." Da k'yar ya iya bud'e bakinsa yace "Na maki alk'awari Amina, Allah ya sauke ki lafiya." Duk da zafin nak'udar da Amina keyi ba hanata yin mumushi ba, sannan tace "Nagode ya Hamza nagode!" Juya mata baya yayi don bazai iya jure ganin Amina cikin wannan halin ba, a haka aka shiga da Amina rik'e da hannun Goggo wadda aka samu aka raba su da k'yar." Goggo kuka takeyi sosai ji take kamar Amina bazata fito ba idan ta shiga. Hamza ya zo ya dinga rarrashinta har ya samu tayi shiru. Minti kusan talatin ana abu d'aya Amina ta kasa haihuwa, har an fara shawarar ayi mata CS don da k'yar idan zata iya haihuwa da kanta. Har sun fara shawarar a sanar da 'yan uwanta Allah cikin ikonshi ta haihu. Su Hamza suna jin kukan jariri suka fara murna suna hamdala. Jim kad'an wata sister ta fito da jariri tana zuwa su Goggo suka yo kanta, Goggo ce ta fara cewa "Alhamdulillah! Ta haihu lafiya." Hamza kuwa hannu yasa ya kar6i babyn yana kallo kafin kuma ya kalli nurse d'in yana murmushi sosai. Nurse d'in ce tace "Ta haifi mace." "Alhamdulillah!!" Shine kawai abinda suke cewa. Kafin kuma Goggo tace "Ina ita Aminar? Ba'a gama kimtsa ta ba mu shiga?" Nurse d'in ce tace "Sai dai kuyi hak'uri..." "Me kike nufi da kalamanki?" Cewar Hamza a d'an rud'e, Goggo ma ta rud'e tace "Bamu gane abinda kike cewa ba." Nurse d'in tace "Abinda nake nufi shine kuyi hak'uri Allah ya amshi kayanshi, ma'ana Amina ta koma ga mahaliccinmu." Saura kad'an Hamza ya saki d'iyar sai da nurse d'in tayi saurin amsar ta, Goggo kuwa in banda salati ba abinda takeyi kafufuwanta kasa d'aukarta sukayi ta zauna da sauri. Hamza zaman k'asa yayi dirshen yana salati kafin kuma ya fashe da kuka kamar k'aramin yaro. "Daman Amina tafiya zakiyi da gaske? Tasha fad'a min mutuwa zatayi na kasa yarda." Haka yayi ta sambatu kamar zautacce a yayinda Goggo ke kuka rungume da babyn. Sai da aka fiddo da gawar Amina lullu6e cikin farin zanin gado bisa gado mai taya a lokacin kuma suka gasgata ta mutu d'in. Wurin ya kuma rud'ewa inda Hamza ya rugo ya rugume gadon yana magana da gawar Amina. Goggo na tsaye tana kuka tana tausayin Hamza, da k'yar aka 6am6are shi daga jikin gadon aka sanya ta cikin doguwar ambulance. Hamza na tuk'i yana kuka har baya ganin gabanshi, ga kukan baby dake k'ara rud'a shi. Can gidan Goggo dake cikin G.R.A suka nufa. Suna isa aka shiga da gawar a cikin gida. Bayan anyi ma Amina wanka an mata sutura sai kuma aka d'auketa za'a kaita makwancinta na k'arshe, gidanta na gaskiya! Hamza na ji na gani ya saka Amina cikin kabarinta, Masha Allah Amina tayi mutane don kuwa har tutse akeyi wurin sakata a makwancinta. Bayan an gama kuma suka juyo gida inda su Hamza suka cigaba da kar6ar gaisuwa. Itama Bilki kullum sai tazo amma bata ta6a dafo komai ba a matsayin abincin sadaka ba hasali ma sai tayi kwalliyarta take zuwa bata nuna wata damuwa ba. A haka aka yi sadakar uku ana zaman makoki, inda Hamza ya dangana yana amsar gaisuwar kowa saidai fa baya magana sai dai yayi shiru ya k'ura ma wuri d'aya ido kamar yana tunani. Ko kuma idan akayi masa gaisuwa sai ya dad'e yana kallon mutum kafin kuma ya amsa gaisuwar. Shikenan Amina ta tafi, mutuwa mai yankar k'auna mai raba tsakani, saidai Allah baya barin wani don wani yaji dad'i. Allah kasa mu dace, Allah kayi mana kyakkyawan k'arshe Amin thumma Amin.
               


EmoticonEmoticon