Wani mutumi ya bauta ma Nnamdi Kanu, ya sumbaci takalman sa - 24gurus.com.ng

Promo


ads1

Featured

Wellcome To 24gurus Blog
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - 24gurusblog@gmail.com

Wani mutumi ya bauta ma Nnamdi Kanu, ya sumbaci takalman sa

Da alama shugaban kungiyar masu fafutukar neman yankin Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, ya kara samun daukaka a idanun magoya bayan Biyafara.

Sannan kuma ga dukkan alamu magoya bayan Biyafara sun fara bauta ma Kanu, wanda suke kira da sunaye daban-daaban kamar ‘mai ceto’ da kuma ‘zababbe’.

A bisa wani hoto da tuni ya shahara, shine na daya daga cikin irin magoya bayansa day a durkusa a kasa yana sumbatar kafar Kanu, yayinda shima ya duka don nuna masa godiya ta hanyar sanya masa albarka.

Ya yi shiga cikin kayan Igbo, harda zani maimakon wando, yayinda yake rike da mafici mai dauke da tambari da kalan Biyafara.

Kalli hoton a kasa: