HAUSA NOBLE'S - 24gurus.com.ng

Promo


ads1

Featured

Wellcome To 24gurus Blog
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - 24gurusblog@gmail.com

HAUSA NOBLE'S

SO NE... PART (9)

Sallama ya faramin na amsa masa, sannan ya fara lallami
na da bani hakuri akan abinda yamini, nikuwa na amsa
masa da cewa kada ya damu ai komai ya wuce ba wata
matsala, a sannan ne ya cemin yanaso nazo gidansa a yau
yanason gani na, na tsaya na danyi shiru ina tunani a
zuciyata 'menene yasa yake nemana' kuma 'me zaimini'
amsoshin da na kasa bawa kaina kenan, sai ya sakemin
magana tare da lallamina, sai na ce masa gaskiya bazan
sami damar zuwa ba, mahaifin Fatima yacigaba da
lallamina amma nikuwa naki yarda, dayaga dae bazan
yarda naje ba sai ya fito ya fadamin halin da Fatima take
ciki kuma ya cemin ba wai shine mai son gani na ba Fatima
ce, kodajin haka sai na amsa masa da cewar zanyi tunani
akai, mahaifin Fatima ya dage da roko na akan najeni
domin kada ya rasa rayuwar diyarsa, a karshe dai da naga
yayi nadama sai nace masa zan zoni.
Bayan mun gama wayar ne na fada cikin damuwa yayin da
na tuna da halin da Fatima take ciki, a wannan lokaci na
shirya domin zuwa Gashua, aikuwa banyi sallama da kowa
ba na je na hau mota na tafi, cikin yamma muka shiga
Gashua da sauka ta daga mota na nufi gidan su Fatima, ina
zuwa kuwa mai gadi ne ya fara tarbata saboda mahaifin
Fatima ya sanar dashi zuwana, mahaifin Fatima ya fito
daga cikin gida sannan ya daukeni a motarsa domin zuwa
asibiti.
Da isarmu asibiti mukaje ya nunamin dakin da Fatima take
muka shiga muka taras da Fatima da mahaifiyarta da take
kula da ita, naga Fatima gaba daya ta rame sannan ko
magana bata iya yi, na kira sunan Fatima a hankali, Fatima
ta juyo a hankali, aikuwa tana ganina tamike zaune tare da
kiran sunana ''yaya Abba'' na amsa mata sannan nace da
ita 'Fatima me ya sameki naganki a cikin irin wannan hali
maras kyau' Fatima ta gyara zaman ta sannan tace dani
'yaya Abba idan har ya kasance za'a rabani da kai to hakan
daidai yake da fadawa mawuyacin hali a gareni, sannan
idan har ba kaine zaka aureni ba to hakan zai zamto tamkar
mutuwa ta ne, yaya Abba inasonka inasonka inasonka
bazan iya rabuwa dakai ba' Fatima ta karasa zancen nata
da kuka tare da fadawa kan mahaifiyarta.
A wanna ranar aka sallami Fatima daga asibiti muka taho
da ni da mahaifiyar Fatima da Fatima da kuma mahaifinta
izuwa gidansu, sannan mahaifin Fatima ya nemi da na
zauna a gidan kwana 2 na amince da hakan, haka na zauna
a gidan koda yaushe Fatima tana wajena muna hira, a
sannan na kara tabbatar da cewar Fatima na tsananin so
na fiye da yadda nake sonta, bayan cikar kwana 2 ne
mahaifin Fatima ya kirani cikin falo inda na taras da shi da
mahaifiyar Fatima da kuma Fatima suna jiran isowata.