HAUSA NOBLE'S - 24gurus.com.ng

Promo


ads1

Featured

Wellcome To 24gurus Blog
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - 24gurusblog@gmail.com

HAUSA NOBLE'S

SO NEH...P(11) # Karshe

Bayan cikar sati guda ne na hada takarduna na diploma
sannan na tafi domin kaiwa mahaifin Fatima, ai kuwa
lokacin da muka hadu da Fatima ba karamin farin ciki tayi
ba, in takaice muku dai a cikin sati guda mahaifin Fatima ya
samar min aiki a Federal University Gashua dake garin ina
kou, shikenan na xama dan garin ga aiki ga karatu duk a
gari daya kuma University daya, na fara aiki da wata guda
ne na fara rubuta project din gama jami'a, bayan na
kammala kuma aka saka ranar aurenmu da masoyiyata
Fatima, ni da Fatima muka kasance cikin tsananin farin ciki
tare da d'okin ganin wannan rana, koda yaushe muna waya
da Fatima sannan duk karshen sati ranar da babu aiki sai
naje wajen Fatima. Tun auren mu da Fatima ya rage sati
guda aka fara shirye shiryen biki, mahaifiyar Fatima ita ta
dauki nauyin kayan da ango da amarya zasu saka, tayi
dinkuna kala uku uku wanda ni da Fatima zamu saka,
nikuwa na gina sabon lungu a gidan kaka ta sannan na
tsara wajen daidai misali akayi plasta aka saka fenti sannan
aka kawata wajen da kayan ado iri-iri. A ranar auren ne tun
da safe yan uwa da abokan arziki suka fara taruwa, a ranar
ne naga yan uwana har ma da wadanda ban sansu ba
muka rankwafa muka dauko motoci muka tafi Gashua
domin dauro aure, muka isa Gashua misalin karfe uku da
rabi sannan karfe hudu nayi aka daura aure sannan aka
fara shagulgulan biki, haka akayi ta shagali a wannan rana
haka muka kwana ko barci bamuyi ba don murna, Fatima
na can wajen kawayenta ni kuwa ina cikin abokaina amma
na matsu da na ganta saidai ba dama, haka aka kwashe
kwanaki uku ana shagulgulan biki sannan jama'a suka
watse, da dare yayi abokaina suka rakoni gida sannan muka
shiga muka taras da Fatima tare da kawayenta muka zauna
abokaina sukai ta mata nasiha har dai dare yayi sannan
suka fita suka barmu ni da Fatima, na fito tsakar gida naga
kaka ita kadai a zaune, nace da ita 'kaka me kike jira har
yanzu da baki kwanta ba?' tace dani 'dama ina jiranka ne
domin na baka abincinku kai da matarka nasan kuna jin
yunwa yanzu' nace da ita 'kaka kamar kinsan dama abinda
ya fito dani kenan' kaka ta dauko kwano guda 2 daya dauke
da farfesun kaza dayan kuma jolof ne na shinkafa sai tirirr
suke alamar ba a dade da dafawa ba, ta bani tace kaje ku ci
kaida matarka. Na karba sannan na juya, ina isa kofar
dakin da Fatima ke ciki ne naji dar dar a zuciyata, abinda ya
matukar bani mamaki kenan, na kasa gane menene dalilin
hakan, da farko dai naga ba yaune muka fara haduwa da
Fatima ba balle nace zanji wani abu a raina, a wannan
lokacine na tabbatar da cewa mata na da wani kwarjini na
daban, nayi kwarin hali sannan na shiga cikin daikin tare da
yi mata sallama. ***