BAZAN AURI DAN FILM BA. Inji Nafisa Abdullahi - 24gurus.com.ng

Promo


ads1

Featured

Wellcome To 24gurus Blog
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - 24gurusblog@gmail.com

BAZAN AURI DAN FILM BA. Inji Nafisa Abdullahi

Shahararriyar yar wasan
Hausa din nan a masana’antar fina-finai ta Kannywood watau Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa ita ba zata auri dan fim ba ko wanene don tana da masoya da dama kuma a ciki ma har ta fitar da wanda take so.
Jarumar tayi wannan ikirarin ne a cikin wata fira da tayi da majiyar mu yayin da take ansa tambayoyi daga wakilin na majiyar ta samu cewa da aka tambaye ta kuma ko me gaskiyar labarin cewa an sa mata biki amma sai kuma aka fasa, sai jarumar ta kada baki tace ita dai a iya sanin ta ba ta san da wannan maganar ba amma watakila masu maganar su ne suka sa mata bikin.
Talla
Ta ci gaba da cewa ita dai abun da ta sani shine ta nada masoya da dama kuma ita tun tuni ta fitar da wanda take so kuma shi zata aura cikin izinin Allah a nan gaba kadan kuma ta kara da cewa shi din ba dan fim bane.