Barcelona tayi magana game da tashin manyan 'Yan wasan ta - 24gurus.com.ng

Promo


ads1

Featured

Wellcome To 24gurus Blog
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - 24gurusblog@gmail.com

Barcelona tayi magana game da tashin manyan 'Yan wasan ta

- Akwai kishin-kishin din manyan 'Yan wasan Barcelona ka iya barin Kulob din

- Barcelona tace babu inda Lionel Messi da kuma Dan wasa Andres Iniesta za su

- Kwanan nan ne dai Kungiyar tayi rashin babban Dan wasan ta Neymar Jr.

A 'yan kwanakin nan aka fara jin kishin-kishin din cewa wasu manyan 'Yan wasan Barcelona za su tashi.


Hakan ya zo ne bayan Kyaftin kuma babban Dan wasan tsakiya na Kulob din Andres Iniesta yace yana duba yiwuwar barin Kulob din. Kungiyar Juventus dai na zawarcin sa. Shi kuma Lionel Messi har yanzu bai amince sa sabon kwantiragi da Kulob din ba.
Wani Darektan kulob din Ariedo Braide ga bayyanawa wani gidan rediyo a can cewa babu inda manyan 'Yan wasan za su je. Kwanan nan dai Kungiyar tayi rashin babban Dan wasan gaban ta Neymar Jr. zuwa Kungiyar PSG kan wasu makudan kudi.

Ku na da labari cewa har yanzu Messi bai amince da sabon kwantiragi ba a Kungiyar. Barcelona ta dai jaddada cewa Dan wasan zai kara kwantiragi nan ba da dadewa ba. Yanzu haka dai yarjejeniyar Dan wasan ta tike ne zuwa badi.