*****MUGUN MIJI PART 2*****

MUGUN MIJI PART(2) . Tayi murmushi. Deena ta fito Antin
nata tace, "ke baki ga bako bane?" Ta dubeshi tace, "sannu
ko," tana hararar sa ta kasan ido.Sam a ganinta ba karamar
tabewa bane ace kamar Antin nata ta aureshi. Deena ta
shiga cikin gida a fusace, anan ta samu Saif da Arfat
kannenta, suna ganinta suka taho da gudu "Ya Deena" ta
rungumesu tana tausayin rayuwarsu tana tsoron halin
mahaifiyarsu, dolene Antinsu tayi auren da wannan kwashe
kwashen da take, tasan ita ba zata hana mahaifiyarta yin
aure ba, to amma Bilal bai kamata ace shine zabinta ba
domin yayi yarinta da yawa duk da cewar ita tana da
shekaru 28 tabbas za'a samu mai shekarunta a 'yan matan
zamani. Shi yasa sam bata so ta nuna Dina tace 'yarta ce,
wai don kar ace ta tsufa. Sam bata son raba 'ya'yanta a jiki
shi yasa bata amince suce mata Umma ko Mama ba sai dai
suce mata Anti. Arfat tace, ya Deena ina ice cream dina?
Tace na manta su a motar Anti bari naji na dauko. Fitarta
keda wuya taga yadda yaron ya kanainaye a jikin Anty,
rayuwarta ta jagule zuciyarta tayi baki taji ta tsani Bilal
tamkar ta kashe shi take ji. Hankalin ta ya tashi ta raina
wayon Antyn tata, kasa karasawa wurin tayi ta dawo cikin
gida. Bilal Idris wani matashi ne mai matukar alfahari da
baiwar kyau da Allah ya bashi, yarone karami dan shekaru
22, dan Unguwar K/dan agundi. Asalinsa buzaye ne, dan
gidan buzaye ake cewa gidansu. Ba masu arziki bane, anyi
ittifakin duk zuri'arsu talakawa ne sai dai akwai su da son
masu arziki, duk inda mai mai yake to suna like da shi. Ya
hadu da Karima ne awani dinner daya yiwa abokansa
rakiya. Da farko Deena ya gani 'yar matashiya da ita ta
bashi sha'awa domin duk jama'ar dake wurin shifa bai ga
mai kyawun Deena ba. Yayi tunanin yasa kai da dadin
bakinsa ya koyar da ita soyayya irin wacce yake ganin itace
wayewa, domin idan ya aureta lallai ya san kila mahaifinta
ya samar masa da abinyi, kila su jawoshi a jiki ya shiga
cikin dukiya yayi kane-kane domin yayi auren jari, sai dai ko
kallo Deena bai isheta ba. Ya fita waje sukayi karo da
Karima ya sume a tsaye don kyawunta yaji shi bai san ana
samun mace mai haduwarta ba, don shi yayi zaton budurwa
ce na tabbata ba mai ganin Karima yace ta taba aure kuma
tana da 'ya'ya har 3, lallai zawarawan zamani ba'a
banbance su da 'yan mata. Ya dubeta yana kashe ido yace
sannu, ta dube shi a yatsine tace yauwa, yace naga kina
zaune ke kadai nazo na tayaki hira, tayi far da ido tace
bana bukata nafison kadaici.Ya sake gyara zama cikin
harshensa na mayaudaran maza yace, "A tunani na duk
mutum mai tunani mai hankali ba zai taba son zama shi
daya ba, dalili na shine zama cikin kadaici na sa damuwa
da yawan tunani, hakan zai sanya mutum hawan jini ko
bugun zuciya". Tace ka gani mutum mai yawan magana bai
cika burgeni ba, haka na tsani mutum mai shish-shigi, yayi
murmushi hade da kashe ido da wani likimo duk na yaudara
kamar yadda aka fi sanin mayaudaran maza nayi yace,
Baby kinsan kina da kyau? Gaskiya koki yarda ko kar ki
yarda na kamu da son ki, zan iya rasa rayuwata ne duk
lokacin da bakinki ya furta Bilal bana son ka. A tsanake ta
mike tana wani irin taku wanda aka fi samunsa a gurin duk
mace mai budadden ido da wayewa. Bilal ya bita da kallo
saboda yadda ta tafi da hankalinsa, ta shiga cikin hall din
da ake party, ta shiga a dai-dai don amarya da ango ne ke
casu, ita ma ta shiga ta taka. Deena na gefe na ganin
yadda Anty ta ke chashewa alhali ga wasu na lika mata
dollas, hankalinta yayi kololuwar tashi, har ga Allah Deena
bata son zuwa irin wadannan gurin takan zo ne saboda ta
san dole Anty zata ki yin wani abu idan har tana gurin.
Lokacin da aka tashi daga dinner, Bilal bai hakura ba ya
nace mata yace, baby zaki tafi baki bani lambarki ba,
sannan kuma baki saurare ni ba, yayi kalar tausayi yace
''idan kika yi haka zaki tafi ne ki barni cikin rudu da tunani,
hakika zuciyata tana sonki. Lallai yau idaniyata zata kasa
bacci zata tsaya cak da aiki. Lallai yau idan na barki zan
bakunci lahira domin rayuwata na cikin hadari''. Zuciyarta ta
buga dam, domin ba abinda takeso face tattali da anuna
mata soyayya, duk kuwa da cewa babu tattalin da ba'a
nuna mata abaya ba wurin tsohon mijinta. Hajiya. Karima
ta figi motarta, ita kuwa Deena ta sunkuyar da kai bata ce
komai ba. Bilal ya koma gida da tunani duk hanyar da zaibi
ya samu Ya ko Kanwar zai bi, domin shi tunanin shi Deena
kanwar Karima ce. Hakika duk yadda hatsabibin matashi
yakai Bilal yaje koma ya wuce nan, domin shi a tarihin
rayuwarsa babu abinda yake so tamkar mace, mayen mata
ne kuma bai taba cewa yanaso ance ba'a sonsa ba, domin
duk yanda zan kaiku ga kwatanta muku yadda Allah ya
tsara halittar Bilal abin ya fi gaban nan 'ya'yan manya dasu
yake soyayya, sai ya gama lalube yarinya zai gudu, dan Bilal
bai san iya adadin 'yan matan da ya taba ba.Ko da ya koma
gida sai rayuwarsa ta jagule yanason ya tuna fuskar Deena,
tsarinta ya burgeshi, to ya zai yi gashi ya furtawa Yar?
amma ko Yar ya samu zai yi maleji idan bukata ta biya ya yi
gaba abinsa bashi kenan ba?. Tarkon so mai wuyar ciruwa,
hakika yau ya kama Karima a makogwaro domin kalaman
Bilal take ji, komai nasa ya yi mata, matashi kosash-she,
lallai irinsa ne zabinta, ai da ta sani ta bashi card din ta, sai
taga kai gwanda ta garashi dan ita tana son taga ana irin
riritata din nan hakan ya sa ta shariya. Bilal sai da ya samu
adireshin din Karima har lambar wayarta ta hannun kawarta
kubra.


EmoticonEmoticon