*** *BARIKI IYAWA PART 16 ***

*** *BARIKI IYAWA PART 16 ***
.
Kwarai,fadi da ihu ki kara da wayyo Allah,,Rausaya take da
kanta,,tamkar wata K'adangaruwa "Sa'adatu nake,,,tai
murmushi da ya baiyana kyawawan hakwaran ta,, ta
rausayar da kai gefe,, kan tace"BARIKI IYWA Ba,,"
ehe."BARIKI ikon Allah ba,ta nuno kanta da hannun ta"Ni
din nan da kike gani na wlh naci dubu sai ceto,, of
course,Karuwa nake,amma A wajen Hafeez,,,. Kara dafata
tayi,kan tace"Ya kamata kisan fa Qawata "BA'A FAFE GORA
RANAR TAFIYA,,sama taka kar kija da BARIKI wallahi,.Dan
ke da kanki kince da Bariki na na shigo,,kinga kenan babu
wani guntun salon BARIKIN ki da zakiyi ya firgita ni..Ta
sauke hannun ta kasa kan ta dan ja baya,,Ki sararawa
kanki,gudun kar ki shiga gona ta,.dan duk tsiya ta bazan
shiga taki ba,.Jiya kin min d'aya,kar ki kara mai maici..
.
Ta dafa kafadar ta ta matso dai dai kunnen ta,kamar mai
rada,tace"Be a good girl.. Ta dana mata hannu,kan tai gaba
tana jujjuya mata wani gu.. Daskare wa tai,tama rasa na
cewa,.Tasan dai a doke, karya take ta daki Sa'a, dan a dire
take, ta fita kauri,sannan komai yinshi take Cikin cire
shakku,.Daki tai,.Tana daura wa da kunce wa,,tana haka
Jummai tazo ita da wata Qawar ta,,Anan Suka lalace suna
kunce wa suna Daura wa, Wai nan duk mafita da zasu ja da
Sa'a suke nema.. Parlour Suka dawo,lokacin Sa'a ta sakko
jera abinci,,tun daga habaicin da suke ta gano su,saboda
haka inda suke ma bata kalla ba,,tana jera abincin ta tana
wakar "Charaman Dudu,.Ta juya tana kada musu bayan ta,,
Suka tafa,Jummai tace. "Fago guda kenan,Tana jin Su,,aiki
ta hau,tana kamalawa ana magriba,tai sallah,tukun ta hau
make up,,ta dakko wasu shegun kaya,,Jeans ne skirt
din,iyakar shi gwiwa, ya dame ta tam,.ta juya tana kallon
bayan nata,,tai murmushi," Ga Fago fa ya fito,,tai
murmushin keta,kai Lalle Jummai, tama bata dariya,.Tasa
rigar Green mai garen hannu,sai Top din na jeans,sanin
Hafeez yafi son ganin gashi a tsefe yasa ta dau damarar
gyara shi,.tai parking din a tsakiya,ta tattare yai doughnut
cif a tsakar kan,ta dau dan kunne barima green tasa,.tasa
flat shoes din ta green,ta kunnan burner ta tsaya a
kai,kayan ta suka dau kamshin turaren,ta kashe ta sake
feshe turare a Dakin da parlourn, ta dau katon hijab da
wayan ta,ta cilla chewing gum a baki,tana kas kas ta tako,
Suka bita da ido,,Har ta sakko suna Binta da ido,,tai
murmushi"Hi Guys,.
.
Da sauri Suka dauke kai,Zahra taja tsaki,,Tai murmushi kan
taja daya daga kujerun dining ta zauna,,K'afa d'aya kan
d'aya ta daura tana Taunar chingum,,Waya ta dakko,ta fara
game,, Zahra ta zungure su Suka ci gaba da tadin su,,.
Shigo war kira ne ya katse ta, ta dubi wayan tana
murmushi,cikin wata mayaudariyar murya tai sallamar,,duk
Suka juyo kallon ta"Assalam Alaikum,.. Tai murmushi mai
sauti dan jin abinda yace,,tace" Allah ja min Ran Namiji
d'aya tilo ga mata biyu,.Tuni ta hau mishi kirarin nata dake
kara fasa mishi kai har ya jima yana waya da ita ba tare da
ya Sani ba,,Murmushi take cikin salon da ita kadai ke Iya
sarrafa lamarin shi,,."Ya akai Toh your Royal Highness,, Da
Girman kujerar ka,,yai murmushi, bakin nan yaki rufuwa,
Sa'a, ta daban ce,shi yasa dan ya kira ta da "Unique, bai jin
kom...
.
Yace"On my way,,mey kika tana nadar min?,,Tai fari da idon
ta, wanda ya kara kular da Zahra,,"Farin ciki,
So,Kauna,,Tare da ni Sa'ada,, r all yours Janeeman,,
.
Ya sauke Ajiyar zuciya, yayin da yake kwana da mota,,yai
horn,mai gadi ya bude,,Duk da taji shi,hakan bai sa ta sauke
wayan ba,ta ci gaba da bashi Hot kalam din ta,,Ta zira
hijab,,Rike da waya ya shigo,bakin nan tamkar gonar
audiga,,hmm,Namiji tamkar wawa ne,mudin ya dace da
mace Yar siyasa,,Bata ko kula da su Zahra ba taje ta Dane
abinta,, cikin hijab din yake kokarin shiga kan tai saurin ja
da baya yaga su Zahra,,huci take tamkar kububuwa,,.Wann
an iskancin har ina?..Ita ran girkin ta bata isa yai mata
hakan ba,,. "Sannun Ku, baki mukai??Ta ruku hannun shi
suna kallon su, Jummai ce tai karfin halin gaishe shi, ya
amsa kan ya juyo kan Sa'a, ta sau mishi murmushi sukai
sama.. Suna hawa ya rukun kumo ta tare da cire hijab din
suna kyal kyala dariya,,Ganin ta a kayan,yasa kawai ya
tsaya jujjuya ta yana kallo,," Wow...U look so Beautiful in
Green tonight..Tai kada ido,tare da sakalo wuyan shi, Tnks
Dear,. Yace shi a kawo mai abinci nan,dan baima son
sauka,.Zahra na ganin ta hau sama da abincin ta kallo su
Jummai, "Ku jirani,,ta tashi tai saman. Tazo bakin kofar,ba
ko sallama,, "Dear, su Jummai zasu tafi,,Ya tsaya yana
kallon Sa'a, ta ajiye cokalin abincin da take bashi,kan ta
tashi," Yi zaman ka,Bari a sallame su Dana Taxi,.yai
murmushi, "yauwa Thanks,.Rigan shi ta dauka,ta Ciro
500,tai yo bakin glass din,.Ta yaye labule,," Sis,gashi a
basu na Taxi,,en kice su gaida gida.. Harara ta maka
mata,taja dogon tsaki,,kan ta juya,dan tasan Tunda ta fada
a gaban Hafeez tofa bazai ba kota ce ya kai,ta juya.a
hankali Sa'a tace "Umma ta gaida Aisha,,.
.
Ta juyo tana murmushi,shi har ya cigaba da cin abincin
shi,dan baida jumurin yunwa. Ranar Juma'a Yace su shirya
zasu gidan su Hajiya,..Zahra keda Girki,.Amma ita a dole
dauki ko Girki batai ba,. Tun alhamis ta soya kajin ta,tana
tashi ta hau pape chicken,,Ta zuba katon flaks,,ta shirya
cikin wani purple da ratsin pink din Swiss less,. Taci make
up kamar mai shirin zuwa zaben Miss Universe,,Sun fito,fir
Zahra tace bazai hau saman ba,Ya mata waya ta
sakko,,.Takun ta ya fara ji,Tuni ya zubawa stairs din
ido,,harda mike wa, Rabon shi da ganin ta tun jiya da dare,,.
.
Wannan k'ayataccen Murmushi ta sau mishi,,taku take
sannu a hankali, tamkar Tausayin Carpet din, Zahra ta dalla
mata harara tare da kau da kai daga kallon ta,Zuwa yai ya
karbi kwandon hannun nata,ba musu ta bashi,ta gyara
gyalen ta tana kallon Zahra,mudin bata gaida ta ba toh sai
dai su zauna haka,tai Murmushi, "Ina kwana sis?Ba tare da
ta kalle ta ba tace" Lafiya, ta kallo mutumin nata,da kawai
Murmushi yake, sosai yana yabawa Sa'a ta ko'ina,bata da
girman kai,bata la'akari da itace uwar gida,tsawan zaman
su bai taba ga Zahra ta gaida ta ba,sai dai ita ta gaishe
ta,ba gajiya wa..
.
shi yasa take kara shiga ranshi,,.Zahra tai gaba,,yana ganin
haka yai saurin zuwa gare ta,, Taja baya tana murmushi,,
"Ina kwana daga nesa,,Ya harare ta," Bana amsawa,,Dama
dazu ma ina kule dake,kinsan zan zo kika kulle kofar ki ta
ciki koh??Tai Murmushi, "So sorry,,yanzu dai muje kaga sis
ta fita,,Ya kara hararar ta kan yai waje,,Suna zuwa ya
danna Remote motan ya bude,,Da sauri Zahra tai gaba tare
da bude gaba,Sa'a tai Murmushi,, Hafeez Yace" Uwar gida
ke zama a gaba Zahra,,Ta kalle shi ta watsar,,"Kai ka
Santa,,nidai ba mai fitar ni nan,,Zai magana Sa'a ta Riga
shi,, "No,Nama fi son Baya Habeebi,,Sis ce ai,,No worry,,Sai
ta zaga kofar gefen da zai na ganin ta ta mirror, ita ai baya
zai fiye Mata gaba,yadda zata kara bata haushi,.Da sauri ya
bude mata,,ta shiga,ya rufe,yasa kwandon a boot,kan ya
shiga,aka bude mishi gate ya fice,,Sai da ya tsaya,ya kwa
saita mirrorn saitin ta,,Suna hada ido ta kashe mishi ido
d'aya,, yai murmushi,,. Tafe suke cikin nishadi,Zahra sai
kokarin tusa magana take,ganin yana murmushi yasa ta
dage,chan dai ta kula,Ashe fa sai ya kalli mirror yake
murmushin,,ta juyo baya a fusace,,Dai dai Sa'an tana mishi
fari da ido kai a langwabe., suna hada ido da Zahra ta yage
mata baki,,Ta harare ta sauke kan Hafeez dake kallon
hanya kamar bai ba,,. Da sallama Suka shiga,Da gudu
Tasleem ta fito,ta kama hannun su, Zahra ta zame," Ni
kauce min,ina Hajiya?,Sai kwa tai kan Sa'a ta kan kamo ta,,
Sai ga nan Hajiyan sun fito da Zahra daga kitchen da fara'ar
ta, Sa'a na ganin ta ta maida gyalen ta saman kai tana
murmushi,,Ta zauna,Zahra ma ta zauna,yayin da Sa'an tai
kasa cikin girma mawa tana gaida ta,, da fara'a ta
amsa,Hafeez ma yadan zamo yana gaida ta,. Suna haka
Abba ya sakko,.Shima fara'a fal fuskar shi,, Tuni Sa'a ta
kara dukar da kanta kasa,,Suka gaida shi,,.Suka dan taba
fira dasu,Yace Hafeez yazo zai bashi sako Suka
fita,,.Hajiyan ta tashi ta koma kitchen, Sa'a tace Tasleem ta
dakko kwandon suje kitchen din,ta cire gyale ta ninke tare
da daura wa a kan jakar ta..Zahra ta tabe baki tare da
gyara zama tana sauya tasha,,.
.
Hajiyan ta dago,Tasleem tace"Gashi inji Aunty Sa'a,ta ajiye
kwandon, Hajiya ta kallo Sa'a, "Bakya gajiya kekam,,Tai
murmushi tare da zuwa ta karbi muciyar," A haba daga
zuwa Baku ko huta ba??basshi Yan nan,na ma kusa,"A ba
komai,zamu karasa da Tasleem, Ta kada kai, " Toh,Allah dai
ya muku albarka, Tace"Amin,,ta fita a kitchen,Tasleem ta
kan kamo ta "Kinji yadda kullum kika kawo abinci yadda
Hajiyan Mu ke yabon ki kuwa?.kai Aunty u r amazing,. Suka
sa dariya,,Tace" Miyar mey za ai??Tace"Miyar kubewa,,Ta
kada kai, ta taimaka mata da bude Leda,,Ita kuma tana kan
kare kubewa,,Ta kunna dayan Gas din,.Ta daura ruwa,ta
yanka albasa ta zuba maggi,,Tasleem duk tana kallon ta,, ta
sa Curry a tafasshen ruwan,Tana gama gurza kubewar ta
zuba aciki,,kubewar tai kyau da ita,,Ta kallo ta "Fadi kar ta
shake ki,tai Murmushi," No naga Taki miyar special, kawai
albasa da maggi kika sa,"zaki ce min baki taba gani ba,.tai
Murmushi "yanxu dai na rike,.amma haka za'a ci??Ta
girgiza mata kai,tare da nuna mata flasks din" Da wannan
za'a ci,.kan 12 da wani abu sun kusa gama wa,,lekowar
Hajiyan biyu,,. Suna daki ita da Zahra, kara take kaiwa,akan
yau Wai girkin tane Amma Sa'a ta dafo abincin fi'ili,,.Ta
kalle ta Hajiyan kan tai Murmushi,, "Ni Zahra na rasa
yaushe kika sauya?.Yanzu kiga fa,ina aiki daga zuwan Ku
ta karba,,amma ke kinyi zaman ki,Kar ki bari ta fiki kirki fa.
Ji tai an ruko kugun ta ta baya,ta juyo,ko Tasleem ce,sai
ganin Tasleem din tai ta fice sai Ogan ta,,Ta dan harare shi,
"Sannu,nazo Taya ki ne,Tai Murmushi," Ai ma mun
gama,,Ni dai sakan ni ko ka manta inda muke?.Ya kara kan
kamo ta,,tace"Allah fa zan sa ma ihu,,Ya fara mata
chakulkuli,,Tuni ta hau dariya,.Shi ya Taya ta har tai wanke
wanke Suka fito,.Tasleem ce kawai a parlourn, nan Suka
zauna su Zahra Suka fito,.
.
Bayan sun gama firar Su gidan su Zahra Suka sauka,,Dakin
auntyn su Suka fara sauka,kan sukai wajen mamy,, Ta tarbe
su da fara'ar su,,Sa'a kawai kallon ta take,Mace ce mai
waye wa,tasha boko,sannan daga ganin ta "Allura batai
halin ruwa ba,dan ba nuna Zahra ta'ta ce,,a yadda Mamyn
ta kula itama Sa'an zatai saukin kai,duk da yar tata na
complain akan zaman su,wanda dama tasan a Rina,,Sa'a ta
fito da Chocolate na coconut parket d'aya ta bawa yaran
k'annen Zahra,,Mamy tai murmushi,a dan zaman da sukai
ta gano Sa'a tafi Zahra sanin siyasar Duniya,, Domin har
wajen da yara Suka bata da ledar chocolate din Sa'an ta
share,,Lalle yarta keda gyara a gaban ta,,.Lokacin da zata
shiga bandaki alwala, akwai dan gidan Auntyn su Zahran a
foo, Yace Mamyn shi ya gama,,Sa'a ta kallo shi,," Tashi toh
na wanke ma,,haka ta wanke mishi ta shiga da foo in
bandaki,,kwarai mamy da kishiyar ta sun ji dadi,.sai
murmushi suke,.Sa'a kam yar siyasa ce,,
.
Gidan Aunty Maryam Suka sauka,,da sallama Suka
shiga,,Habeeb yana mota a parlourn, yana ganin su ya taho
da gudu gun Sa'a,, Hafeez har mamakin sabon shi da Sa'an
yake,Da sauri ta ware mishi hannu," Oyoyo Habebee
nah,,Aunty Maryam ta fito tana musu dariya,,Sabanin Zahra
da ba yabo ba fallasa,,Suka zazzauna,Hafeez yana"Sister
kodai zaki bamu Habib ne??Tai murmushi tana kallon Sa'a,,
Mai D'a wawa ne,indai zaka so nashi,toh zai so ka,, "Wa zai
Iya da kiriniyar Habib Bros?? Sa'a tace " Mukam a
bamu,zamu Iya,ko Habeebe??Ya daga mata kai,, Nan Suka
gaisa,,yaran ta suka zo,kai Familyn Hafeez sun mata,kowa
ka gani da fara'ar shi, a zaton ta bazata samu tarbar nan a
wajen su ba,ganin yadda akai kan tazo gidan,amma da
mamakin ta kowa yana maraba da ita yanzu,,.Yadda take
son Hafeez, dole taso Familyn shi,shi yasa a siyasan ce
take siye su,.Da zasu tafi Tace su biya zatai ma su Fodio
siyayya,Yaji dadi kwarai,dan bai kawo wata siyayya a ranshi
ba,,Tasan tsofi akwai son Turaruka,.Nan ta jidar
musu,Drinks ne,da sauran kayan tsaraba,. Zahra har abin
ya daina bata haushi,mamaki ya dawo bata,,wato tana
nufin ta ma fisu son dangin nasu ko mai?? Biyar Suka yada
zango a Family House din su,su Fodio yai murna da ganin
iyalin Hafeez din, Kowa ba nuna waraki ya tarbe su,,Nan
Suka yada zango,ta zage tare da sakin jikin ta dasu,,Kakar
su Hafeez kadai ta rage,Itama duk ta tafi,,.kwarai sunji
dadin tsarabar,duk da dama Hafeez din yana kyautata
musu ta bangaren sutura,da dan abun masarufi,,Yara suna
ta murnar chocolate,. Sai bayan Isha'i Suka nufo gida,Fir
zahra taki zaman Gaba,har dariya abin ya bawa Hafeez,.
Da mamakin Sa'a taga sun baude, Layin su ya dauka,Dan
murna harda rukun kume shi,.


EmoticonEmoticon