HAUSA NOBLE'S

2.GANGAR JIKINSA NA AURA P2 NA JAMILA UMAR TANKO
(JUT) Malam
Habu da *yarsa Hanne suka bi motar dakallo
har ta hau titi ta kure sannan hankalinsu
yadawo kan kayansu. Malam Habu ya kalli
*yarsa Hanne wacce hawaye ya gauraye
idanuwanta dakumatunta, abin ya bashi
mamaki ganin Hanne nakuka alhali kuma ita
take son karatu take murna dazasu taho, ya
sake juyowa sosai ya kalleta yagahawaye ne
ke zubowa daga idanuwanta dayanabin
daya, ya ce "*Yar Baba, kukan me kike yi?
Karki cemin yanzu bakya son makaranta
bayan keaka kira fadar mai gari aka
tambayeki kika ce kinaso. Ba'a son raina ba
nima na kawo ki makarantarnan ke kika
amsa musu. Shine kuma yanzu kikekuka?
Idan kinsan bakya so to ni a wajena tafinono
fari sai mu juya kafin mu shiga ciki. Kansila da
mai gari su suka tilastamin in kawo ki amma
badanhaka ba nima bazan rabu dake ba na
kawo ki nanuwa duniya, babu wanda kika
sani. Hanne tagirgiza kai cikin shesshekar
kuka ta ce "Baba bamakarantar bace bana so,
rashin kunyar da masumotar can suke yi
maka shine ya sani kuka. Malam Habu yaji
hawaye ya cika masa ido amma sai yajure
yayi murmushin karfin hali ya ce "Allah
Sarki*yar Baba, babu komai duniya ce. Duk
wanda yagagirman tsohon wani, za'a ga
girman nasa. Hakakuma duk wanda ya raina
tsohon wani sai an rainanasa, zamani ne ya
canja babu sanin girman Allah, ko an hada
mutum da Allah kamar an hadashi dasa'ansa,
wani cewa zaiyi daina hadani da Allahkarka
cuceni Wa'iyazubillah. Ya ci gaba da
cewa"goge hawayenki 'yar Baba kizo in dora
mikiakwatin mu shiga ciki kada dare yayi min
kinga harla'asar tayi. Tasa gefen gyalen da
taci damara dashi ta goge idanuwanta kana
ta matso ya ciccibiakwatin karfen nan ya dora
mata a kai shi kuma yadauki bokiti da katifa a
daya hannun sa'annansuka juya suka doshi
cikin babbar kofar shigamakarantar, yaci
gaba da yi mata nasihohi masuratsa jiki yana
nuna mata wannan abin da aka yi masa a
gabanta ya zama darasi a wajenta
duklalacewar tsoho koma ba tsoho bane na
gaba da itakada tayi masa fitsara. Ta zamana
ko a ina takekuma kome ta zama ta girmama
na gaba da ita.Ta zama mai taimakawa
mabukata, kasancewartasan talauci ta kuma
dandanashi tana kandandanashi. Masu gadi
uku suka iske a bakin kofarshiga cikin
makarantar, suna zazzaune, MalamHabu yayi
musu sallama gami da mimmika musuhannu,
Hanne ma ta duka ta gaishesu, bayan sun
amsa, Malam Habu ya ce "Yarinya na
kawomakarantar nan, ta ina zanbi mu shiga
ciki? Dayadaga cikinsu ya ce "Mikewa zakuyi
sosai zaku tararda ofishin Malamai dana
shugaban makarantar.Malam Habu yayi
godiya suka wuce, har sun danyonisa suka ji
masu gadin nan sun kwalla musu kira bayan
sun dawo, sai daya daga cikinsu ya
kallesusama da kasa ya ce "Dan Allah Malam
muna datambaya sai bayan da ku ka wuce
tambayar ta fadomana. Malam Habu ya gyara
kayan dake hannunsagami da yin murmushi
ya ce "To Allah Yasa na sani.

Read More

HAUSA NOBLES

1.GANGAR JIKINSA NA AURA P1 ⃣Wata kwarababbiyar
mota kirar
bus mai kararfatattakekkiyar salansa ce ta
tsaya a bakin get dinmakarantar 'yan mata ta
gwamnatin tarayya dakegarin Kazaure, wato
F.G.G.C. Kazaure. Tana tsayawakondastan
motar ya ja kofar ya bude "Barararaa"saboda
kwankwatsewar da kofar motar ta yi
sakamakon cin ruwa da gafje-gafje da tsabar
tsufa.Wani dattijo mai kimanin shekaru
saba'in da doriyane ya fito, da wata *yar
yarinya tana biye dashiwacce shekarunta
basu wuce shekaru goma shadaya ba, Bayan
sun furfito kondastan motar yazagaya baya
wato but ya dauko wata katuwar akwatin
karfe irin ta *yan makarantar wacce akadafka
sunan mai akwatin garza-garza da fenti
bakiHANNE HABU IMAMU. Ya ajiye gefe ya sake
janyowata karamar katifa wacce take daure
ya doraakan akwatin, sannan ya dauko wani
bokitin karfesabo dal yana sheki shima an
fenteshi da sunan mai bokitin wato HANNE
HABU IMAMU. Daga karsheya mayar da kofar
but din ya rufe ya juyo ya kallidattijon wato
Malam Habu ya ce "Baba baka fa cikamana
kudin motarmu bafa, gashi har kun
sauka"Malam Habu ya sake marairaicewa ya
ce "Dana daAllah fa nake hadaka kuyi hakuri
kudin da yayi saura a aljihuna ko gida bazai
mayar dani ba, sai nanemi ciko kayi hakuri
dan Allah, dan haka nemanace ta zauna a
maleji yanzu baza ka tausayawatsoho ba,
karbi arba'in din?" Kondasta ya sakefusata ya
ce "Dalla Baba kana bata mana lokaci
gafasinjoji har sun fara tsaki sun kagu suma
a kaisu inda zasu. Ka zauna kana mana
magiya tun dazumuma fa ba'a bati muke
shan man motar da mukejigilar nan bafa, da
kasan kudin motar taka bai cikaba me yasa
ka hau? Har zaka ce wai yarinyar amaleji ta
zauna, maleji ba cikin mota bane? Bakasan
har a sittin muke daukar na maleji ba daga
inda muka dauko ku zuwa nan nayi maka
ragi nace kakawo hamsin dinma gashi kaki
biya sai wataarba'in ka bani, kai wallahi Baba
saika ciko managomarmu kaji ko? Direban
motar dake zaune awajen tuki wanda yake
jin duk abinda suke yi, saiyanzu ya waigo
inda suke yayi magana ya ce "K.b wai yane?
K.b ya ce "Har yanzu wannan tsohon baidaina
magiya ba wai shi ayi masa ragin goma
kudinyarinyar nan data zauna a maleji,
Hamsin nace yabiya, ya wani bani arba'in.
Kuma ma dan raininhankali harda cewa
kudin aljihunsa bazai mayardashi gida ba,
wato yana da kudin, cikawa ne bazai yi ba.din
aljihunsa bazai mayar dashi gida ba,
watoyana da kudin, cikawa ne bazai yi ba.
Malam Habuya danji dadi ganin direban yayi
magana ko zaice abar masa amma sai yaji
kalamansa sabanintunaninsa gara ma abinda
kondastan ya fada masa,cewa yayi in har
bazai biya ta dadin rai ba to zasu farka
aljihunsa su dauki gomarsu, Malam Habu
yarike baki don mamakin irin wannan
rashinmutunci, can ya nisa ya ce "Allah Ya
kyauta, bari nabaku kudinku abin duk bai kai
ga haka ba, yasahannu a alhihunsa na dama
ya dauko watacukurkudaddiyar naira biyar ya
sake saka hannu a aljihunsa na bangaren
hagu ya dauko gudar nairaashirin da
kwandaloli guda biyar, ya hadakwandalolin
nan guda biyar da cukurkudaddiyarnaira
biyar din nan ya mikawa kondosta ya
ce"Gashi dana Allah Ya kiyaye. Ba kunya ba
tausayintsohon nan yasa hannu ya karbe
yana gunani "Daman kana dashi ka tsaya
kana bata mana lokaciduk fasinjoji sun kagu,
direba ya juyo ya ce "YayaK.b ya baka, sun
cika? K.b ya ce "Eh sun cika jamuje

Read More

*** *BARIKI IYAWA PART 12* ***

*** *BARIKI IYAWA PART 12* ***
.
Baban ya shiga dashi ciki,yai wa mama magana,,ta fito da
kamalar ta,Ya dan duka ya gaida ta, itama da fara'ar ta ta
amsa,,kan tai dakin Sa'an da ta koma bacci,,. Ido waje take
kallon shi, tunda mama tace tana da bako ta sa hijab,ta
zata Ali ne,dan tama manta da Yace safe,,ido 1 ya kanne
mata,, dai dai Baba ya fito zai tafi,yai mai sallama,, Ya
dawo da kallon shi kanta,,Ta zauna tana mai mamakin jin
sallamar shi da Baba kamar sun San juna,," Ina kwana,, yai
mata wani kallo, ta kauda kai tana murmushi,,A hankali
tace"Allah sa ma kai break irin wannan sammako,,ta dan
harare shi,, yai murmushi,Tare da kama ciki, halamar
yunwa..Ta make kafada,,ya marai rai ce fuska,,"Wajen
Baba nazo,kuma na dace,,harma ya ban auren ki,harda dan
duko kai a hankali kamar mai rada,,Ta kara dukar da
kanta,,kan ta tashi ta debo mishi abinci,,ta zauna,,kunun
gyada ne mai cous cous, yasha madara da lemon tsami,sai
Doya da kwai,,Ya kalle ta yana nuna dakin mama,,yana yin
halamar kar ta fito,,Tai dariya,,Ya dau cup din kunun yakai
baki yana kara kallon dakin mama,ita dai sai dariya take
mishi,,ya rintse ido,dan jin dadin kunun,ita kwa da sauri ta
waro ido, ya bude ido a kanta,fuskar shi ba yabo ba
fallasa,zatan ko bai mishi dadi bane,Yace"Hope ke kika
dama,,ta
.
** *SOME PAGES IS MISSING* **
.
Ta daga mishi kai tana sunne kai,, "Tunda Baba ya sanar
dani zuwan ka da abunda kazo nema wajen shi na amince
maka,,." Hafeez, buri na ka cika a gun Abba,,Ta kallo shi,"
I'm inluv with you than I ever was...I love you too Hafeez,,
Da sauri ta rintse idon ta da murmushin kunya, dan jin wata
kunya da bata San tana da ita ba ta rufe ta,, Kallon ta yake
yana murmushi,, kai shikam baiga abunda Sa'a ta rage shi
ga mace da yake son aure ba.. " Kunya " "Addini: "Class"
Kyauu " Da Iya kwarkwasa.. Shikam ya gode Allah, Sa'a ta
mishi komai da ta so shi.. "Tnks much My Unique,,Yaushe
zan turo a mini Tambaya?? Baki ta fara kunshe wa tana
dariya kadan kadan,Tuni ta so zautar dashi,.. Yau sun buga
luv,tamkar kar su rabu, Dakyar ta samu ta gudu gida dan
magriba tayi,,Ashe haka "So" din yake??..Ashe Haka
masoya suke ji amma a baya take ganin wautar su??..ita
kam indai haka ne,toh itama sai ta sarrafa zuciyar ta, dan
gujewa so mai zafi,,Ji take kamar dama ta girma ne da son
Hafeez,,
.
Mama ma sai da ta gano yau Sa'a na cikin farin ciki
matuka,,Dan komai ta ke sai kaga tana murmushi ita
kadai,,. Shikam daga nan wajen Zahra yaje dan cika
hukuncin Hajiyan shi,Da Tasleem ta sanar mata murna fal
ranta,Wai yau Hafeez ne yazo gidan domin ta??.. Suna
zaune bayan ga gaisuwa ta kasa ce mishi komai,dan jinsu
take wani iri.,Shikam kallon ta yake yaga ta ina ta Gaza,,
sannan mey Sa'a ta fita?..Ya kada kai,, "Amm Zahra
magana nazo muyi ta fahimta,. Ta kallo shi fuska
sake,,.Yace"Nasan kinji maganar ba ke kadai zan aura
ba,,ina fatan tun yanxun ki rike ta yar uwar ki tun kan azo
ga batun zama,,dan Sa'adatu she's simple, baki da
matsalar zama da ita.. Tuni Annurin fuskar ta ya kau,,tai
tsagal ta mike," Ya Hafeez kar muyi haka da kai,,Ban San
wata Sa'adatu ba kai na Sani,,sannan ni kishiya,wallahi
kishiya na dauke ta, ba Wai yar uwa ba..akan mey an gama
magana tashin farko ka watgazan tsari..Kallon ta kawai
yake yana murmushi,, Sa'an shi kawai yake tuno wa,mace
mai Iya lafazi da kawai ci,,Akallah a haihuwar kaji zai haifi
Zahra,amma dan fitsara shi ta tasamma aka tana mishi
haka..Kyale ta yai sai da tai mai Isar ta harda
hawaye,kamin ya taka mata birki.
.
Tuni ya hade rai,, Yace"Bafa shawarar ki nazo nema ba da
zakimin fitsara,aure na da Sa'a kuwa zan Iya cewa shi yafi
zame min dole,,so tun wuri kisan inda kika dosa,dan gaba
bazata mana kyau ba,,.Nan ya barta tana ta kuka,A ganin ta
magana ya fada mata, wato ita auren ta dashi bai zama
dole ba??,,.Mamyn tata ta shigo dakin ganin Ta fito daga
parlour tana kuka,.Lalle yar ta tana da aiki a gaban ta
ja,don tana son tusa kanta a inda bata kwarjini, tasan
tabbas kukan ta bazai rasa nasaba da Hafeez ba,, Gashi ta
nace da sauran dangi sai anyi auren nan,amma tana
tausaya wa rayuwar auren yar tata data ki jinin kishiya
...
Soyayya ake yi tsaftacacciya a tsakanin Hafeez da Sa'a, a
yanxun kam ya maida gidan su Sa'a kamar gidan su, tun
yana jin nauyin zuwa har ya ware,,sai dai abu 1 dake kawo
musu cikas Ali,,Ali ya nace sai Sa'a,, tashin farko yazo da
Baban shi Wai a bashi Sa'a,, kai ranar tai dariya har taji ba
dadi,,sai a ranar ta kara tabbatar da Lalle Ali ba tsaran ta
bane,, duk da Abban yaso tun wuri hakan ta faru,bai rufa
wa mai gidan nashi ba ya sanar shi Sa'a Nada Miji,,sai dai a
bawa Ali hakuri,,dake shi Dattijo ne mai dattako ya amince
da Allah baiyi Matar shi bace,amma shifa Ali fir yaki daina
zuwa,,duk da ko yazo ba kula shi take ba,da yaga baci ya
dawo gori,inda alkawari ai Baba bazai ki bashi auren ta
ba,kodan muhallin da Abban shi ya basu,,Take Sa'an
tace"Indai wannan gidan kake wa toh ka kwantar da
hankalin ka,amma aure ne ka kara lalata shi,dan ka nunan
kai ba na kwarai bane,kuma dole mubar muku gidan Ku...
gori har yaje kunnen Baba,.Tuni ta bawa mutanen da suke
mata haya Notice, ta hau gyaran gida,,shi Baban bai zata ta
dau zafi haka ba,,sai ranar Laraba bayan anyi da wata tazo
Wai gobe zasu tashi,,da fari Baban dariya yake mata,sai dai
ganin ta fara parking yasa ya tsayar ta,,"Sa'adatu ba fa Ali
ya bani gidan nan ba,kinga bai kamata muyi wa Alhaji haka
ba,, tace"Baba ai ko ba gori yaci karan nan ka yarda mu
shiga gidan nan, Ina da gidan zama,amma fur kunki zama
ciki,sai dai nasa haya,Baba chan gashi na zamani,nan na
kasa,ya kamata inn ka samu dama Baba kai amfane
ta,,kawai ce mishi zakai tashi zakai,daga baya ni nasan
abin yi...Duk da haka Abban bai yarda ba,sai dai kamar
yadda ta fada Washegari ta dakko mai katuwar Daf, Baban
baya nan aka fara kwasar kaya,sai gidan Sa'a,, gida ne mai
daki Uku,,biyu kana na,daya katon parlour, duk da baida
wani girma,amma na bulo ne,kuma na zamani,daya dakin
mai bandaki a ciki nan ta jera wa su mama kayan su da
gadon ta,tasa aka sa carpet a pparlourn da manyan
tuntu,,sai fridge da Katuwar TV,,Ita kuma ta hular da katifa
da sauran tariki cen ta..Lalle gaya wa mai zuciya,bamai
Dukiya ba,,,sai da kudin account dinta yai kat..
.
Baki sake su Baba suke kallon Sa'an,basu isa musu ba,dan
har kuka ta sau musu,,Mama ta lallabi Baban,,ta kira
Fadeela ita tazo,Gidan ya musu dai dai,Dan tsakar gida ne
mai dan fadi kadan,anyi mishi siminti,suna da ruwan
su,komai dai dai sauki akwai shi,Fadeela ma tai farin ciki
sosai,,. Da yamma Baba ya sanar da Alhaji cewa sun
tashi,yai hakuri abinne yazo musu a bazata,,yai mishi Allah
sanya alkairi, ai gida kam nashi ne duka,zai yi duk yadda
yaso,sai yazo ganin gida,,.yaji dadin yadda ya fahimce shi
kwarai,yai mishi kwatancen inda suka koma,.kan ya dawo
yana fada ma su mama yadda sukai,Sa'a tace Baban ya
bata mukullin tsohon gidan toh,za ai mishi aiki,zuciya 1 ya
bata,yana mai shi musu albarka. Tai ma Hafeez text, cewa
sun tashi da address, dan tasan zai Iya zuwa bai same su
ba,,5da rabi kuwa yazo, yana ta yiwa mama murna,,da
Allah sanya alkairi,, Nan take sanar shi ai Sa'a ce ta tada
ballin sai sun tashi,ba shiri,,yai murmushi, Yace "Toh ya
kikai da yan hayar cikin??Da mamaki take kallon shi, Ya
akai yasan nata ne?,Sai da suka je parlour yana yaba tsarin
gidan,komai a saukake, amma da kyau,,yadda suka zauna a
Chinese carpet din ma ya kayatar shi,ya jin Gina a tun
tun,kamar wani basarake,,nan ta sanar mishi abinda Ali
Yace, " Shine na basu Notice, bawai kora na musu ba,tana
murmushi, ya kada kai, "Good,kin min dai dai,nan din tunda
ba na uban nashi bane naga kafar mutum,,Tuni ta hau
kunshe baki tana dariya,,Fadeela ta shigo suka gaisa,yana
mata itama Allah sanya alkairi,.. Alhaji yazo daukan Fadeela
yaga gida,,yana ta son barka,,nan yai wa Sa'a zata ga
gudun mawar shi,,. Ko minti 3 ba ai da tafiyar Fadeela
ba,Ali yazo,Baban shi ne Wai Yace yazo yaga gida kan
suzo,,Allah yasa baban baya nan,Sa'a tace ya jira ta a waje
toh,,Da dariya suka fito,da ka gansu kasan suna cikin
nishadi,in ran Ali yai dubu ya baci,,a zuciyar shi yana,,"shifa
kota ya ya sai ya samu Sa'a, atoh, yama ji da kyau,,.
.
Ba ko magana ta mika mishi key, Ya karba yana kallon ta,,.
Hafeez Yace" Ganan keys na gidan naku,,an bar muku shi
sarkin yan gori,,en ya zamo last da zan kara ganin kafar ka
a gidan nan,, dan bazata mana kyau ba,,Suka juya Sa'a na
daga mishi hannu da shakiyanci,,ya kulu Iya kuluwa,,.
Direct Baban shi ya kaima key in,,. Washegari sai gashi
yazo da kanshi ba'asi,, Baban ya kira Sa'a,ba ko dar ta
korowa Alhaji bayani,kan danshi ne ya Goran ta musu,Alhaji
ya girgiza kai, "Sa'a in banda abinki, ai ni nai kyautar nan ba
Ali ba,,Ya ajiye musu kan ya basu hakuri,tare da sanar shi
zai ga Alin. Sa'a sun gama schl,sai Attachment,Zancen aure
sai karfi yake,yayin da Zahra sai baudewa take,Da son abun
Sa'a take attachments din,daga dan wannan sukai sha'awar
daukar ta bayan ta gama.. Ansa bikin su zuwa Hafeez din
ya gama ginin shi,,Duk bangaren kowa na shirye shiryen
biki
.
Matsala 1 da ta fara fuskan ta shine kana nan maganganu
da dangin Hafeez suke a kanta,,dan sau daya da ya taba
kaita ta gano basa yi da ita,,tun daga ranar ta kudiri wani
abu a ranta,burin ta kawai Allah kai Damo ga harawa.
Makarantar zama da Miji mai mata ta bazama nema,,duk
wani wa'azi mai kyau da ma'ana, mai taken mallakar Miji
Sa'a Nada shi a waya,,duk wasu littattafai da tasan tabbas
zata kara Sani akan su ta neme su,, Matakin farko data fara
shine Bincika yanayin kayan Dakin da Hafeez yake da
muradi,cikin wasa sukai abinsu,nan kwa bai son satar amsa
tai ba,,a haka in fira tai dadi a wasa da wasa sai da tasan
mai Hafeez yafi so na daga abinci, sutura,color, best
perfumes da sauran su,,kan ma ta shiga ta gama karantar
daga A har Z.. Tanan tai wa Zahra zarra tun kan su
shiga,ita kullum batta dabara sai ta yaya zatai Hafeez ya
zama nata ita kadai??
.
Duk abinda aka sa mishi lokaci toh tabbas zaizo da
sannu,babu wanda yakai Hafeez da Sa'a farin ciki, duk da
Zahra tana farin ciki, amma Sa'a ce ta tsokane mata
ido,,ganin har yanxun yadda yake rawar kafa a kanta,duk
da tayi nasarar sanya dangi yadda da cewa Lalle Hafeez
zai auro musu karuwa,,kuma tabbas sun yarda,,. Hakan
yasa dai dai da lefen ta a dangin Hafeez din sai yan tsirirai
ne suka kai,,yai kaya na azo a gani,duk dunsu ba
banbanci,,,Ware kunya Sa'a tai ta hau gyaran kanta da
kanta,,.Tsohon gidan su sukutum ta maida gidan gyaran
ta,Tun kamin sati da biki ta kammala duk wasu jeka ka
dawo na hidimar ta,,ta hada nutsuwar ta waje guda,,dan
kwarai tunda taji wa'azin Malama zuwaira ta dau
darasi,,don tabbas itama ta fahimci yawancin amare basa
cikin nutsuwar su ake kaisu gidan Miji,,kenan duk wani
gyara da za'a miki kadan ne zai tasiri a gare ki,dan komai
yana bukatar nutsuwa.. Kaflas din fenti babba tasa aka
nemo mata madarar shanu,dan tasan takamar da za'a
gwada mata kenan su Zahra, dangin Fulani,tasha tai wanka
..,sai da tai ta wankan amare na Lalle kullum a daura Dana
madarar shanu da turaren Durot,,,Wata kwararriya ta
samu,tazo har gidan tana biyan ta,,su fresh Nonon Rakumi,
Su ganyen Tumfafiya,tai,duk wani sirri ta nemo su ta hada
anyi mata,kan satin biki yazo in ka kalli Sa'a tamkar wata
yar black Indian nan masu kyau,sai shining jikin nan
yake,ga wani dan karan kamshi da laushi da fatar ta
take,,kai kace daga Maiduguri ta fito,,Dan tun kan biki tasa
wata Qawar ta yi mata hanyar wani mai hada turarurrukan
mata masu kyau da kamshi,,Dan ita akwai son
kamshi,musamman na turaren wuta.. Yau Juma'a, ta kama
gobe za'a dauro auren su Hafeez da Matan shi,sun shirya
kyatattiyar Dinner,, Kowa ya halatta Sa'a kawai ake jira,,in
kaga ango sai wage baki da ido yake yaga ta ina zata
ratso,,Zahra an hakimce a kusa da Hafeez, an Gaji da kyau
itama,,gashin nan an zubo shi baya,duk da taiwa Hafeez
din kyau amma shi burin shi yaga Sa'an shi,,duk sunyi
waya tace suna wani room ne a hotel din 5 mint's,,
.
Hargowa da fadin MashaAllah shi ya juyar da hankalin
Hafeez da Zahra,,tafi ake mata,ganin gasu Tj yan kanan
Bodyguards dinta na unguwa sunyi wankan bakaken suite,
kowa yasha bakin glass,yaran sunyi kyau matuka,sun
shassha kunu su a dole masu tsaran Aunty Sa'a, sai abin ya
kayatar,Ga nan Qawayen ta yan karya da wanda sukai
Turkish suma sunsha kyau,,sanye take cikin wata doguwar
Riga ta net Golden da ratsin Orange,, sai ta temaka wajen
kara haskaka mata fatar tai wani yellown kyau,,ga wani
arnan Hill Orange da Pose ,,sai dan mayani data rufa a
gefe,,Fuskar nan ta Gaji da kyau,Ko Zahra sai da ta firgita
ba Hafeez, dan tunda biki ya karato ta fara gyara da dogon
hijab da Nikaf take fitowa su gaisa..tayi kyau ainun,,ga
wani tsadadden murmushi da take sakar wa,sabanin Zahra
da ta nemi fara'ar ta ta rasa,,Hafeez ya tafi duka,,A ranshi
fadi yake"Tsarki ya Tabbata ga Allah,, Ya ma manta da
jama'ar hall din kamar an tsikare shi ya tashi,ba ko kunya
yai wajen ta,,tana ganin haka tai saurin dukar da kai tana
murmushi,Tuni aka hau flashes ta ko'ina,, in ran Zahra yai
dubu toh ya baci.., haka suka jera har mazaunin su.

Read More

*** *BARIKI IYAWA PART 11* ***

*** *BARIKI IYAWA PART 11* ***
.
Dakyar Abba yasha kan Hajiyan,ita sai fadi take batace
haramun bane,,kawai Zahra take so ita daya..sai da ya
burkice mata kan suka dai dai ta,,Zahra ai zabin ta ce,.Da
Zahra taji tuni kuka ya karu,,shikenan kuma. Da Yamma
Zahra ta tartara inata ina ta zatai gida,,ta kudiri kuma ba ita
ba kara zama gidan su Hafeez Wai dan shi,,lokacin da suka
fito baya nan, kuma sarai tasan dan su ya bar gidan dan kar
ya kaita,,ga Drivern Abba sun fita,kawai suka je a tsayar da
Taxi,,itama da kyar suka samu da mace a ciki.,,Yace zai
kaita kan ya kaisu,,a rashin babu suka shiga,,har akaje
unguwar da za'a ajiye wacce suka tarar a Taxin,sun zo
zasu wuce wata a tsaye da wani da yai musu kama da
Hafeez a tsaye sai murmushi yake,,ta motar ta daga wa ta
tsayen yatsu tana kiran "BARIKI Ba..Zahra ta kalli Tasleem,"
Ba ya Hafeez bane wannan kuwa??..da sauri suka kara
juyawa,akai Sa'a dai dai itama Sa'a ta daga wa ta motar
yatsu,ya dan juyo ganin Taxin da ta wuce,sai dai baiga na
ciki ba,,Tasleem tace"La,wallahi shine Aunty Zahra,, tuni ta
cika ta batse dan gane da wa yake tsaye,wato itace wacce
zai gama su tare??mai Taxi na yin kwana ya sauke dayar
suma suka sauka,Zahra zatai kwanar Da sauri Tasleem ta
ruko ta,,"mey zakiyi Aunty Zahra?? Ki bari man muji wacece
tukun mu karasa tunda wannan ta San ta,.sai a sannan ta
dawo hankalin ta, mai Taxi Yace in bazasu tafi ba su bashi
kudin shi, da sauri suka sallame shi suka bi bayan Kaltum
da zata shiga gida,,. "Baiwar Allah,, ta juyo da fara'ar ta"
Aa,Baku tafi ba?sukai yake, "eh, tambaya muke pls?ta
gyara tsayuwa," toh muje daga ciki,Zahra ta kada kai,
"Aa,muyi anan,." Dan Allah wace wacce muka wuce yanzu
da wani a tsaye kika daga mata hannu?tai murmushi, "au
Wai BARIKI?? Yar Duniya ake fada miki,badai saurayin ki
bane ba koh?Tasleem ta kalli Zahra da ke mai maita sunan
BARIKI.
.
Dake uwar surutu ce tuni ta hau fadi ba'a tambaye ki ba,."
Ai in saurayin ki ne toh wallahi ki hakura dashi,dan ba mai
Iya ja da BARIKI a fagen nan,,indai har ya shiga hannun
BARIKI toh sunan saurayin ki "Sorry ",nan ta hau basu
labarin irin kasa wasu da tai da samarin su,Ku harda Matan
aure bata bari ba,,campaign na siyasa tai kadai aka mallaka
mata dankareriyar mota da katon gida,tuni suka waro
ido,,.ta cigaba" wallahi ina baki shawara ki ma bar
mata,duk da batta gwani ita..haka tai ta basu karya da
gaskiya,tuni Zahra ta tsure,Tasleen kira take "Shikenan yaya
ya hadu da karuwa,.ji yadda yake wage mata baki,.bata
Ankara ba sai gani tai Zahra na hawaye..tai Dede kwanar
tana leken su,, a dai lokacin da Sa'an ta miko wa Hafeez
waya,sai wani yauki take irin na yan Duniya.. Yayin da
gogan baki tamkar gonar audiga,,dan ko bata furta ba a
formular da Kunal ya bashi ya gano da son shi a tattare da
ita,,dan yau ba hade rai, mai makon haka ma sai murmushi
take mai dan cike da kunya,. Ina,Zahra in ta cigaba da
tsayuwa a tana kallon su zata Iya hawan ruwa,tuni ta juya
Tasleem ta daura bayan ta tana waiwayen wannan
BARIKIN, kai ko ita ta tafi da imanin ta wallahi,, duk ba Wai
kyau tafi Zahran ba amma da gani ta fita sanin kan ta
Duniya..sai dai ba yadda za ai Yayan su ya kaso musu yar
BARIKI.. Tab, bari suje gidan. Gidan su zahran da ba'a je ba
kenan sukai gida,in banda hawaye ba abinda Zahra take,
Tasleem tayi tayi ta kasa dai nawa,. A parlour suka tarar da
Hajiya,itama ta tsunduma tunanin Wai Hafeez da mata
2,,kukan Zahra ne ya dawo da ita,,tuni ta hau tambaya,, kan
Tasleem tace komai Zahran ta amshe,tana kuka tana
tsarawa Hajiyan. " Kuma Wai yar BARIKI fa Hajiya?da sauri
ta waro ido waje,,tace "wallahi Hajiya Wai ma sunan ta"
BARIKI,Tasleem tace"Hajiya kinga yadda yake mata dariya,
tamkar wacce ta mishi ishara da Aljanna.."Ni ya ishe ni
haka,,ni dama nasan yaron nan ba haka kawai yake
ba,,Ashe yana chan an dauke hankalin shi, kuma Wai
Karuwa yar BARIKI?? Ta kallo Zahra,"yi shirun ki,bari baban
naku yazo,,bazata sabu ba Sam,,da hankali na bazaa auro
min sirika yar BARIKI ba wallahi..
.
Hafeez na dira gida Hajiya ta fara sauke mishi,,da tsananin
mamaki ya sauke kai kasa,yasan bai isa wanke kanshi da
Sa'a ba yau a wajen Hajiya,.."Saboda ta dauke maka
hankali har ka gagara ban bance tsakanin Aya da
Tsakuwa,,Yace"Hajiya Wallahi ba haka Sa'a take
ba,,wannan sunan daban,kuma.."Rufe min baki shashasha
kawai,, in baka Sani ba toh ka Sani yanzun,Zahra kawai na
Sani,ba ruwana da da wata BARIKI,Macen kwarai ce za'a
kirata da sunan BARIKI ta amsa??. Mita take har Abba ya
ritsa ta bayan ya dawo,,yana hawa ta bi bayan shi. Hafeez
ya juyo yana hararar Zahra da Tasleem,,"Yaushe na zama
abin wasan Ku da har zaku Bini a baya?? Sukai
tsurutsuru,ya nuno Zahra da yatsa, "Bari ma kiji,wannan
abun bazai hanani auren Sa'a ba,sannan Gobe kisan nayi ki
tattara ki koma gidan Ku,,.Ya tashi yai daki,,ta bishi da
ido,Tuni ta fara hawaye,abun harda gori? Ita kwa mita
tsinana a zaman gidan banda takaici?Bari taje gida,har
gidan Aunty salma zata,karya ne a gama ta zaman aure da
wata,,. Shikwa yana shiga daki ya jawo waya,ita kanta
Sa'ar haushi take bashi,,dan dazun suna tsaye Ali yazo,,
saboda tsabar rashin so Wai tace mishi " Excuse me"?,.
.
Tai wajen Ali,duk da bai ji mey suke cewa ba,amma ya
gano wanda suke waya dazu ne,tuni koh ta kanta bai bi ba
ya shiga mota..shine kuma yana zuwa Hajiya ma ta sauke
mishi,.Yai dan tsaki, Lalle sai ya dage,,Ashe da gaske take
Wai Bai karbi soyayyar taba? Toh ya take so yayi??Ya fidda
zuciyar shi kan Yace"Sa'adatu I luv u,komai??ya sake
tsaki,,a hankali ya furta "Sa'a matsala,.. Ita kuwa tunda taga
Hafeez ya zuciya ta rasa sukuni,gashi ta kasa kiran shi, a
nata tunanin ajin ta zai zube,. Tai kwafa,amma Alin nan sai
ta sa kafar wando daya dashi zai ki yayi zuwa wajen ta, in
takamar sa gidan na uban shi ne,toh itama tana da gidan
daya taka wannan na bulo ma..ta kara tsaki,,ta juya ta dau
waya kan ta tashi zaune..tai dailing numbern Hafeez din,da
sauri ta katse,," Oh God,,ta rike kai,"Wai Sa'a mey ke damun
ki ne akan Hafeez??Tun farkon haduwar su da Hafeez
shine kadai Namijin da ta taba mafarki,,shine kadai wanda
ta taba chachar baki dashi dan Dabarar ta takare, shine
kadai ke sawa ta bata lokacin ta wajen tunanin shi, Shine
kadai a yanzun in suna tare take jin wani nishadi kadan
kadan na shigar ta..Sannan yanxun yayi fushi ta damu,ji
yadda take gwara kan maza,manya da kana nan su,,yau 1
wanda taki jini ya hana ta sukuni.." Ya Ilahiii", "Mey kenan
hakan yake nufi?? Ta kalli agogo 9,kwanciya tai kamin ta
hau Mishi text da bata San ma ta fara ba..Da sauri ta goge
na ban hakuri ta rubuta. " Shine ka tafi ba koh sallama??
Tasa halamar shagwaba.. Tai murmushi, kan ta kishingida.
Text yaji ya shigo wayan ya kara tsaki kan ya kwanta,chan
ya jawo wayan,dan yana zata koh Alert ne na contact na
Zane da aka bashi,,da mamakin shi yaga Sa'ada,.yai
murmushi, take yaji kuncin shi ya yaye,tuni yai reply.. Taji
text itama,tai murmushi dan tasan shine,."Munyi fada ai,, tai
murmushi da har hakwaran ta suka fito, tai rufda ciki kan ta
mishi Reply.. "Ai bama fada..Triple sorry" .
.
Shima yai rubda cikin yana karanta wa,,yai murmushi,,"No
banyi ba..ban Aron minti 5 naji muryan ki sai nai sorryn..ya
tura..chan itama ta bude,,tai murmushi tana duba sling,,
kan ta kada kai tai reply"An baka. Ringing 5 tai kan ta katse
ta dauka da sallama,,yai Jim,,tace"koh ba'a yafe ni ba??ya
sauke wata ajiyar zuciya,, kan Yace"u know what?? Kina da
dadin muryar sosai,,Tai murmushin jin dadi,. Kan tace
"kaima haka?..sai kuma ta datse harshen ta da hakorin
ta,bata ma San ta furta ba,,yai murmushi,." No,ke ai ta
daban ce,,Tace"Koh,? Yai shiru,"Sa'ada waye Ali nan ne??tai
dan murmushi,, "Dan mai gidan Baba ne,,Yace" ehm,sai mey
kuma??ta kada kai "shikenan, Yace" Ba So??tai Jim, kan
tace"akwai,.tuni ya mike zaune,,sai ta kara da"Shi yake
kayan shi amma,,ya sauke wata ajiyar zuciya da taji ta,,
Yace"Toh Ni fa Sa'a?? Tai shiru tana,tace"Hafeez ne
kai,Yace"ehm?Toh ana son Hafeez din?? Tai Jim,gaban shi
ya fara faduwa,,ita kwa murmushi take a hankali,. Sai da ya
kara magana,"Ko har yanzu ban karbi Son ba Sa'adatu??
Wallahi believe me,I am madly, deeply in love with you
...Sa'a I really Love you, en u know?? Tun farkon haduwar
mu na kamu da son ki,sai dai a wancen lokacin ban San so
bane Sa'ada, nasan dai ina tsananin kishi na ganki da gyale
shara shara,,sai naji zuciya ta na tafasa,,in na tabo ki
mukai ne kawai nake samun relief.. Tunowa take da lokacin,
tabbas tun ganin Hafeez na farko ta ji sauyi a tare da ita.
.
Ya cigaba, "Kin tuna ranar da na watsa miki lemon
strawberries a jiki??? Tuni ta rintse ido dan tuna wa da
wannan rana,ba zata manta ba har kuka tai,,.ya katse ta"
nasan ke a zatan ki dan tsokana nai,,Ya girgiza kai, "Ganin
mai shagon nan fa nai yana ta kallon ki sai ga kin dame
Riga,ga nan gyale a kafada,,shine yasa na tashi na harare
shi yana sosa kai,kan na baki baya na watsa miki,nasan
Ummi ta gani,en dole ki nemi agaji,sai kwa gashi ta baki kin
suturce jikin ki da abayar ta,,.Jin shi kawai take..ta katse
shi da" Mey zakace da Marin da kamin kuma??Ya sauke
ajiyar zuciya,, "Sa'adatu.. Taji kiran har kwakwalwar ta,.,"
Naga shigo war ki kina ta wani yauki,,ga kayan sun dame
ki,ga wani Wai shi gyale da kika dakko kin maka shi a
kafada,baki sa maraba da wacce ta fito haka,,ga duk kusan
ke ake kallo,,amma ke na fuskan ci baya ma damun
ki,haka kika kutso taron nan kika shigo fa,,da zaki kula,da
zaki gano tsabar haushin da nake ji, hararar ki nake tayi ko
zan samu saukin zugin raina,,ina fa jin wani a yan uwan su
Ummin yana cewa wani "Woow,,she's Beautiful!! Kamar na
cire babbar Rigar Aminu na rufa miki naji,.sai dai nasan ba
laifin shi bane,,naki ne,. Dan na rage zugin dake raina na
koma baya,,juyo war da zanyi naji ki kusa dani,kuma kamar
ki shige min jiki,,bazan boye miki ba,a lokacin nan ji nan
kamar ma na rufe ki da duka,,dan na tsani mace mai
chudanya da maza,.ban Ankara ba naji saukar sanyi a jiki
na,,...Yai shiru tare da rintse ido,,." Sa'ada ban so tuno
Marin nan da na miki,, duk da har gobe kowa yana kallon
kece kika mare ni in kika cire Ummi da Aminu,tanan kawai
na gode Allah. Tai ajiyar zuciya,, Lalle sai yanxu ta kula da
kishin da Hafeez ke nuna wa,,ya katse ta,, "Da fatan kin
gamsu zaki yafen,..yaji shiru,, Ashe kudin ya kare.. Shi
yana ta zuba ko warning din bai jiba,,ya dau wayan Glo ya
kira..dai dai zata kira..
,
Yace" kiban dama gobe nazo gida da safe,yanxun dare
yayi,. Ta kada mishi kai,,"Ok.. Yace"Mey toh zan samu??tai
Jim,dan bata gane nufin shi ba,,sai tace*Sai dai kazo
gobe,,Yace"Promise?,, ta kada kai "Promise.. Haka suka
sallamar kowa ya kwanta da tunanin Dan uwan shi..barin
Sa'a yau da taji duk wwani haushi ta daina ji na Hafeez,, a
ganin ta ko a haka ya barta ta gamsu da Lalle So ne ya
Jawo Haka.
.
Tun safe Zahra tai niyar gida,.ko jiran Tasleem batai ba,,
tana zuwa ta zube a tsakar dakin Mamyn nasu,, Aunty
Sadiya ta kallo ta,"Lfyr ki kuwa??Kinzo kin wani zube min
ba koh sallama??Tuni ta marai rai cewa Mamyn tasu tana
hawaye,, "Mamy,,Na shiga 3 wallahi,,.sai ta barke mata da
kuka,,Da jin haka ta waro ido waje,, Ta tashi ta kamo yar ta
ta,tasan dai tatsuniyar gizo bata wuce ta koki, Amma sai ta
tambaye ta" Meye kin shiga 3??
.
Nifa ban son wautar nan taki ta yan fari?? Ta lafe jikin shi
tana kuka,,"Mamy Wai Fa Hafeez mu 2 zai aura,, kuma ya
rasa da wacce zai hadani sai yar BARIKI mamy,, Mamyn tai
Jim,ita dai dama wannan hadin na Zahra da Hafeez kwata
kwata bai mata ba,,duk da Hafeez da yake a gurin ta,amma
tasan ba abunda yar tata zata tsinta a gidan shi sai ciwan
rai, toh amma ita batta da wani power a gidan,tunda itace
auta a cikin gidan su kakanin Hafeez din,, haka itama aka
mata wannan auren hadin,, gashi za'a sake da yarta tilo
mace,dan duk sauran kannen Zahra maza ne,,. Rarrashi ta
fara,,"Toh meye ne abun kuka anan Zahra?Ta sake magana
cikin kuka"Mamy Abban su fa Wai ya yarda,,Hajiya ce kawai
tace bata yarda ba,, Dan Allah mamy ki Taimaken ki samu
Fodio da maganar,tunda Abban yana jin maganar shi,,.
.
Ta sake fashe wa da kuka"wlh mamy ban son zama da
kishiya.. Da sauri ta kwade mata baki,,ta rike bakin tana
cigaba da hawaye "Wato kaddarar ki a hannun ki take koh
Zahra?Ta hade fuska mamyn,,"Da hankalin ki kike furta irin
kalaman da wanda basuyi makaranta ba kadai ke fadan
shi??tai kwafa,"Sannu autar mata,,Toh ki sata a
ranki,,sannan ki daura damarar zama da ita tun yau,.Da
sauri ta kalli Mamyn nasu,, "Anya mamy kuwa tana son
ta??,,Bari Abban yazo,shi zata tsara mishi komai ya shige
mata gaba,,.kamar tasan tunanin yar tata,,sai ta dawo mata
Nasiha,,kan tana saukaka kishi,dan duk yadda ka dauki
Kishiya toh fa a haka take zuwa maka,," Ki duba ni da
auntyn Ku,da yawa mutane basa gane kishiya tace,dan
tsabar muna zaman mutunci da girma ma juna..ki cire
wanna akidar taki tun wuri Zahra,,Dan kin fini sanin halin
Hafeez, bare akan abinda yake so,,sannan duk Family nan
suna matukar yaba dashi,hakan yasa suka zaba mishi ke
suna ga da hankalin Ku zai zama daya..kar ki fara bata
rawar ki da tsalle tun yanzun,, tai ta mata,amma ina,ita
gani take Mamyn bazata gane ba,. Karfe 9 da rabi yana
gidan su Sa'a,, ita duk daukan ta wasa yake,yai katari kuwa
Baban su yana waje,,Har kasa ya gaida shi cikin girma
mawa,. Da fara'a Baban ya amsa,,Take yaji Hafeez ya
kwanta mishi,dan ba kasafai yaran yanzun suka Iya girma
ma manya ba haka..Ya kalle shi da fara'a, "Hala ka wani
kake nema??Ya sunkuyar da kai kasa cikin girma mawa,, Da
halamar kunya Yace"Baba dama wajen ka nazo,,Yace" Toh
mu shiga daga ciki,Ya Sosa kai,Daga zaure ya cire musu
farar kujera,suka zauna,sai leken cikin gidan yake ko zai
hango sahibar shi,,Baban ya dan kula da hakan,"Allah dai
yasa lfy?Ya sunne kai kasa cikin kunya,"Amm Baba sunan
Hafeez, muna chan kasa daku kadan, dama,Amm,Sa'adatu
na gani Baba,shine nake Neman izinin fara Neman auren ta
a gun ka.
.
Baban yai murmushi, a ranshi yana ambaton "Allahu
Akbar,,Lalle zabin shi Dana Sa'an shi Yazo,,Dan duk wanda
zai cika sharudan mulunci na Neman aure Hafeez ya
fara,.Bai manta zancen shi da Sa'a ba akan Tara samari ba
na aura,,bai manta amsar da ta bashi a lokacin ba,," Baba
duk saurayin da ya fara zuwa Neman aure na wajen ka toh
ya cika sharuddan aure na,,ka shaida hakan Baba,,nasan
zaka fini sanin dawa na dace Baba..Da irin kalaman nan
Sa'an take kara shiga ranshi,, ga daga gani daga gidan
mutunci Hafeez din ya fito,,Ya kada kai, "Tabbas kayi
abinda ya dace Hafeez, hakan ya nunan daga gidan da ka
fito,,Allah yasa alkairi a ciki,,.Tuni ya fadada fara'ar shi
yana sunne kai,, Baban ya tambaye shi iyayen shi,ya dai
gamsu da duk bayanan shi,sai kuma bincike ya rage.
.

Read More

== RAYUWAR NIHILA 6 ==

== RAYUWAR NIHILA 6 ==
....... KARSHEN LABARI.......
.
Ya sameta ta na daki ta rufe kanta da mayafi yazo ya yaye
yanata murmushi ta mishi itama yayi hugging abunsa kam
kaman wani zai kwacce ta yace alhamdulillah my love yau
Allah ya cika mana burinmu Allah ya barmu tare har gaban
abada tace ameen ya kawo musu yoghurt da kaza da tace
bazata ci ba yace inaa bazai yuwu ba saitaci yayi feeding
dinta sosai sannan suka tashi sukayo alwala sukayi sallah
bayan sun idar ya kama kan ta yana addua sannan ta tashi
tace ita bacci takeji ta sako er lingerie dinta ta kwanta
gogan naku ya je yayo shiri shima ya kwanta ya hugging
dinta ta baya can dai yaga ba zai iyaba ya fara nuna mata
kalan nasa son taji zuciyanta ya fara bugawa abunka da
new comers shagwaba ta fara yi baji ba gani akan yayi
hakuri amma sam hisham yayi nisa kissing dinta yake ta ko
ta ina yana fada mata kalaman da ita kanta batasan da su
ba nidai na rugo a dari na kulle musu kofa amma fa haly
qawata tace bata yarda ba inje in gano mana kwakwaf ta
tankade keyana na koma saidai kash abun gama ya gama
faruwa na dawo inata cizon yatsa asuba ta gari NihilSham.
.
After 5 years
.
Najma najma najma wai ina kika shiga ne sarkin rigima fito
yau saina zane ki sarkin barna najma ta fito make a bayan
daddyn ta yace mommy we are sorry tace bawani ai dama
kaike biye mata kullun tayi ta barna a gidan nan ai saina
zaneki tayi narairai da ido ta sakko taje gabanta ta rike
kunne ta naa mummy I'm sorry bazan kara ba daddyn ta
yace common we are sorry give us a smile suka bita da
gudu zasu mata cakulkuli tana daria hisham ya bita daki
yayi hugging dinta sosai yace I so much lov u my nihila tace
i love you too my happiness my love and life Allah ya barmu
tare yace ameen na jawo musu kofa na kulle taku har iyau
har e jiya har e shekaran jiya har e kullumbis salamm...
.
Mun zo karken wannan dan gajeren labarin ... Mekuka
fahimta ko ince wani darasi kuka sama?

Read More

LABARAN QASA

Babu sabani tsakanin Buhari da Osinbajo -
Gwamnati

Fadar shugaban Najeriya ta ce babu wani sabani tsakanin
Shugaba Muhammadu Buhari da mukaddashinsa, Farfesa
Yemi Osinbajo.
Matakan da Osinbajo ya dauka na gaggawa wurin tunkarar
matsalolin da kasar ke fuskanta tun bayan tafiyar Shugaba
Buhari hutu, sun bai wa masu sharhi mamaki.
Kuma hakan ya sa wasu na ganin ya yi wa mai gidan nasa
zarra a wata dayan da ya shafe yana lura da al'amuran
kasar.
Sai dai fadar gwamnatin kasar ta ce duk wani yunkuri na
nuna cewa Osinbajo ya fi Buhari "kokari ne na kawo rudani".
Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan
harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu, ya ce 'yan adawa
ne kawai suke son kawo rudu ta hanyar kimsa wa mutanen
tunanin akwai rabuwar kai tsakanin shugaban da
mataimakinsa.
Sanata Ojudu ya ce "Kusan a kullum sai [Osinbajo] ya
tuntubi Shugaba BUhari saboda akwai abubuwan da ke
bukatar hakan. Ina nufin yana neman shawararsa wajen
zartar da manyan hukunce-hukunce."
Ya kuma kara da cewa irin ayyukan da Farfesa Osinbajo
yake yi yana yi ne domin ya burge Shugaba Buhari ya kuma
nuna masa cewa zai iya gudanar da al'amuran mulki ko da
shugaban ba ya nan.
Tun dai ranar 19 ga watan Janairu Mista Osinbajo yake
shugabancin Najeriya a matsayin mukaddashi sakamakon
bulaguron da Shugaba Buhari ya yi zuwa Ingila domin ya
huta sannan likitoci su duba lafiyarsa.
Daga lokacin kawo yanzu dai, mukaddashin shugaban ya
zartar da wasu ayyuka da ake ganin sun kawo sauyi a
kasar musamman ta fannin tattalin arziki.
A makon da ya gabata ne ya umarci babban bankin kasar,
CBN da ya zuba miliyoyin daloli a kasuwar hada-hadar
kudade, al'amarin kuma da ya sanya darajar Naira ta dan
farfado.
A baya dai Shugaba Muhammadu Buhari ya hana yin hakan
da manufar karfafa darajar kudin kasar.
Har wa yau shugaban ya yi hakan ne domin dakile shigo da
kayayyaki daga kasashen waje wadanda ake ganin za a iya
yinsu a cikin kasar.

Read More

LABARAI DA DUMI-DUMI

Rikicin jagorancin jam'iyar PDP bai kare ba

Dangantaka na kara yin tsami tsakanin bangarori biyu da ke
jayayya a kan shugabancin babbar jam`iyyar adawa a
Najeriya, wato PDP.
Bangaren Senata Makarfi ya yi tir da matakin da Senata Ali
Madu Sherif ya dauka na bude hedikwatar jam`iyyar, bayan
wani hukuncin da kotun daukaka kara a kasar ta yanke, har
ma ya zargi jam`iyyar APC da rura wutar rikicin PDPn.
Jam'iyar APC ta musanta cewa ta na da hannu a cikin
rikicin cikin gidan jam'iyar adawar.
Haka ma bangaren Ali Madu Sherif, shi ma ya musanta
zargin banagaren na Makarfi.
Yanzu dai sai kutun koli kawai ce za ta iya yanke hukunci na
karshe kan wannan danbalwar.
To amma kuma 'yan Najeriya da dama na tambayar kansu
ko yaushe ne wannan rikici na jam'iyar adawar zai kawo
karshe?

Read More

*** *BARIKI IYAWA PART 10* ***

*** *BARIKI IYAWA PART 10* ***

.
Sai bayan magriba ta tashi,.har lokacin Shima yana
nan.,tun fitar ta yai musu sallama,,sai dai da mamakin shi
tana ta tada mota taki tashi, sai tsaki take kamar ta rufe
motar da duka,,sai dai ba hali,,yai murmushi kan ya karasa
wajen,,ta dago kai ta kalle shi kan ta cigaba da abinda take,
yace"May I?ta dago,da har zatai gardama, kuma dai sai ta
fito.
.
Shima yai yin Duniya taki fitowa,, ya fito tare da rufe
motar,duk ta wani marai rai ce mata,har magana take mata
kamar mai jinta,shi dariya ma take bashi,,yace"Muje na
sauke ki, ta kallo shi,ta girgiza kai taga yana murmushi,sai
ta kule.tace"No tnks,, kan ta kauda kanta gefe..ana haka
Aminu ya fito za shi wani gu ya dawo,,turus ya tsaya kallon
su,," Ya na ganku anan?Baku tafi bane?ya kallo Hafeez
daya harde hannu kawai yake kallon ta,, tai dan tsaki"taki
tashi ne,,ga dare nayi,.ya kalli Hafeez, "Toh ka sauke ta
man,in yaso gobe na taho miki da ita in an gyara,,ya kallo
ta," ko ya kika ce?sai ta dan sachi kallon Hafeez din,,"Nifa
Aminu da dai..ya katse ta "ki saman a mota,, yai baya kan
ya bude motar, ta kallo Aminu,, ya daga mata kafada
halamun bata choice,. A mota duk ta takura kanta,,ta gyara
gyale, ta murza zobe, da sun hada ido tai saurin dauke
nata,,ganin yadda ya wani seta mirrorn yana facing nata,shi
dai sai murmushi,ya dan kallo ta lokacin da yake kwanar
wani gu,," zan karbi sako pls,, ta kalle shi tare da kada kai,,
Ya karbo suka fito da mutumin,, wanda zai bashi kwangilar
Zane na gini..ya kallo shi, "mutumin kace da amarya kake
tafe?da sauri ta kallo shi, ya wani kashe mata ido.. Yace"
Madam ina wuni,.da yake ta amsa,.tana nanata amarya a
zuciyar ta,, bari ya shigo,,ta kauda kanta gefe,har ya
shigo,.ya kalle ta yana daura belt,"Muje koh? tai mai banza,,
yai murmushi,, ta kallo shi, "Nice amaryar? Ya kallo ta yai
dariya,," no, ta kada kai "yauwa,.ya sake kallo ta" Uwar gida
ce ai,,da sauri ta kallo shi,, ya daga gira,,"yes,.
.
uwar gida ko kinfi son amaryar? Tuni ta hade rai,. "Malam
kaja ni ko ka sauke ni,,uwar gidan wa??Shima ya hade
fuska kamar gaske,,"uwar gida na man,baki ta sake,tama
kasa furta komai,ga ya wani hakimce ya tsare gida,,kawai
ta juyar da kanta,,.sun kusa zuwa wayan ta yai ringing,, ta
duba number ne,sai da ta kusa tsinkewa kan ta daga,a
gadaran ce ciki ciki take maganar,," wane Alin?.. Tai Jim,ta
kallo Hafeez din, Shima ita yake kallo yana kallon titi, sai ta
waske dan ta bashi haushi"Oh,na gane,ya akai toh?..wayar
ya warce dai dai sunxo kwanar daza ta kaisu gida,,ya kai
kunnen shi a kai kai ce,,"Tana tare da mijin auren ta ne,, kai
hakuri ka Adana Tarihin sunan ka,,ya kashe wayar tare da
ajiye wayar bai ko kalle ta ba yai parking,. Lalle man din nan
akwai karfin hali!..baki sake kawai take kallon shi,,wannan
irin tusa kai haka,.jin bata fita ba yasa ya kalle ta, shi take
kallo,yace"na sauya miki ne hala??ta maka mishi harara
kan tai waje,.da sauri yace"wayan ki,.ta warta, zata fita ya
dago glass din.."wannan fa?Shima ta warce,kan tace "ba'a
Sani ba,.sai kuma ta manta jakar ta,. Ya kunshe dariya,,
tuni ta kara kuluwa,.zata shiga gida ya fito yace" Sa'ada,.da
sauri ta juyo da zummar masifa,,jakar ya mika mata yana
murmushi,. Sai kuma dafe kai"Ya salam,.sai kunya ta
kamata,,toh saurin mey take haka??ta tako zata karba tare
da juyar da kai ganin yana murmushi,. Maimakon ya
bata,sai yai baya da ita,ta juyo ta kalle shi, suna hada ido ta
dauke kai,."ban man,.yai shiru,,ta sake kallo jakar ba tare
da ta kalle shi ba,yai murmushi, "Toh yaushe zan dawo?ta
sake kallon shi a kai kai ce,." Kamar ya??da abinda ya rage
kuma?ya kada kai, "kwarai,da abunda suka rage da yawa,.
Ta kallo shi da rashin fahimta ,,ya daga mata girar shi,." Ai
in kinga abubuwa sun kare,toh tabbata uwar gida ta
tare,.gaba daya kamar an kulle mata baki taji,. Ta sake
mika hannu ya kautar, "in kina son na baki ki fadan yaushe
zan dawo??da kaguwa tace" Gobe,.sai kuma tai shiru,.ta
rasa meye dalilin kasa kallon idon Hafeez da tai,.murmushi
yai,kan ya mika mata jaka,.tana karba da sauri ta arche
gida.
.
Harta shiga yana Binta da kallo,ya sauke ajiyar zuciya,.Lalle
ba makawa a kamu da ciwo,wanda yake tunanin koh shine
So din,.ya sake ajiyar zuciya kan ya tada motar shi yana ji
da nishadi. A bangaren ta itama haka,kwance take sai juyi
take a gadon ta,ta rasa dalilin da yasa yanzu ta daina jin
zafin shi kamar kullum,ga wani dan karan kwarjini da ya
fara mata yanzun da da bata gani,, ta furzar da iska kan ta
kara juya wa dayan gefen, buguwar zuciyar ta ya tsanan ta,
lokacin da ta tuno yadda yake mata wani kallo wanda ta
kasa fassara shi,, kai ta girgiza, tana mai rarrashin
kwakwalwar ta da ta daina tunano mata Hafeez,. Tai adu'a
tare da gyara kwanciya. Shima hakan ce ta faru,.sai juyi
yake a katifa, sai yayi kamar ya kira ta,sai kuma yai
murmushi, a yau kam,ya rasa nutsuwar shi, ga wani fara'a
da yake tamkar gonar audiga,ya duba agogo,8 da wani
abu,ai dare bai ba,. Waya ya dauka ya danna kiran
Aminu,.yana dauka ya fara mishi tsiya,"Tsiyar gauro
kenan,bai gane dare yayi,,yai dan karamin tsaki,"Gargadi
zan ma Malam, wallahi BARIKI ya fita a bakin ka,ka kirata
da Sa'adatun ta sak.. Dariyar keta ya fara mishi, har sai da
yaga ya fara kuluwa ya dan sarara, "I knew it,.
.
Dama nasan Biri yai kama da mutum,,kuma ance in kaga
Kare na shinshina Takalmi,toh dauka zai,Lalle Abokina ka
afka da yawa,.ya cigaba da dillika dariya,Hafeez yace" kai
fa dan iskan gari ne,mey na afkawa dayawa? Yace"Son Sa'a
kuwa,da sauri yace"So?yace"kwarai kuwa,tun farkon ganin
Sa'a nasan ka afka son ta,amma ka tsaya a haushin ta ne,.
Shidai Hafeez mamaki yake,tunda ya kashe waya yake
murmushi, Ashe sone hakan?Toh amma ya akai bai San So
ba shi?abu daya ya Sani yana da muradin auren Sa'a,. Tuni
ya dau waya ya fara tsantsara mata Text,a lokacin da itama
bacci ya gagari idon ta, kwakwalwa ta kasa daina turo mata
hoton Hafeez.,Ji shigowar Text yasa Ta bude ido,takai
dube kan wayan,ta mirgina ta dauko,tuni taji bugun zuciyar
ta ya karu, duk da murmushi take yayin karan tawa,
"Hafeez.. A hankali ta furta,,kan tai tsam tana tuna wani
abu,.
.
Washegari kowa ya tashi cikin farin ciki,musamman
Hafeez, duk da bata mishi ko reply ba,amma yasan ta ga
sakon shi, har Hajiya sai da ta kula da hakan,binshi da kallo
kawai take,, ya zauna a kujera.,lokaci lokaci yana dan duba
waya ko zaiji shigo war amsa.."Ni Hafeez, yau ko mafarkin
Aljanna kai ne haka?Yai murmushi, "ko daya Hajiya,.ta
kada kai,. Ana haka su Zahra suka fito ita da Tasleem,suka
gaida shi,ya kallo Zahra,yana tunanin mey yasa bai jin
komai game da Zahra irin na Sa'a??..ya lumshe ido, Sa'a
kam ta daban ce..da sauri ya bude ido jin Tasleem tana ga
abincin shi,.
.
Zahra sai satar kallon shi take,Hajiya na kula dasu,ba tasan
mey aibin Zahra ba a gun Hafeez, duk irin zaman da zatai a
gidan bazai taba kallon ta a Wai wacce zai aura ba sai dai
qanwa,kai shi manta wa ma yake da wani batun auren ta,,
koda kuwa zai aure ta, toh gini ma na mata 2 yai,daya a
sama da turakar shi,daya a kasa da dakin yara,kai da kaga
gidan kaga na zaman mata 2,. Hajiyan ta kalli Zuhra tai
mata halama da hannu suje daki,.ta yafico Zahra sukai
chan,kan ta kallo Hafeez,." Wai ina zancen mu ya tsaya ne
Hafeez??.. Ya kallo ta da rashin fahimta,. Ganin haka yasa
tamai ta gwari gwari,"zancen ka kai da Zahra man,ko har
yanzun baka fahimta ba?? tuni yaji gaban shi ya fadi,sarai
yasan Hajiyan su akwai zafi,musamman akan lamarin
family, yasan bai isa cewa bazai auri Zahra ba yanxu,dan
yana son Sa'adatu,, sai dai yana tsoron hada Zahra da Sa'a
a matsayin Matan shi,.. "Hafeez,. Tunanin mey kake haka
ina magana??..Ya Sosa keya," Am Hajiya,yana nan, sai dai
dama ina da magana..da sauri ta daga mishi hannu,,"idan
har maganar auren nan ne,toh anyi an gama Hafeez,
.
. Ba zaka maida mu ya'yan ka ba fa,.Yace"Bashi bane
Hajiya,.Amm dama wata ce naga, kuma,.kuma..ya kasa
karasa wa, ganin yadda Hajiyan take kwada mai
harara,,."kuma mey? eyeee, nace Kuma mey?kana nufin ka
fasa auren Zahra dan kaga wata bare chan??ko mey kake
nufi??.Da sauri ya girgiza kai, "aa ba haka nake nufi ba,,..
Dama,sai yai shiru ganin Abban su ya sakko,ya sunne kai
yana gaishe shi, da fara'a yake kallon shi,."Mey kuma ya
faru Kaida Umman taka nake jiyo fadan ta tun a sama
haka??Tai kicin kicin da fuska,,"Ka zo dai ka jiye wa kunnen
ka,dama duk kai ne mai daure mishi ai,,toh wallahi karan
nan bai isa kauce wa auren Zahra ba,,yai murmushi, kan ya
kallo Hafeez," Ya akai Hafeez?? Ya kallo Hajiyan da sai
harara take binshi dashi,.ya fada mishi yadda sukai da
Hajiyan, "kuma fa Abba ni duka zan aure su fa,,..A zabure
Hajiyan ta tashi," kana nufin mata 2 zakai??!ya sunkuyar da
kanshi,,ta kalli Alhajin, "ka dai ji da kunnen ka koh?ta nuno
Hafeez," Toh baka isa ba,babu wacce zaka hada da
Zahra,,Abban yai mishi halamar yai shiru,,ta kallo
Alhajin,"kafa sa baki, dan karan nan zamu bata da Hafeez
kwarai..tai sama tana bam bami,.
.
Zahra da tazo jikin kofa tana zatan zancen auren su zatai
mishi Hajiyan ta soma kuka,, Tasleem ta taso,"lfy Aunty
Zahra?Ta zaunar ta akan gado,,"Tasleem mey na rasa da
Ya Hafeez bai sona ne Wai??duk zaman nan dan shi nake
yi,amma banda amsa gaisuwa ba abinda ke shiga tsakanin
mu,,shine yanzu zai ce zai hada ni da wata ya aura dan
tsabar rashin so??.,,,, ta barke da kuka abin
tausayi,Tasleem tace"Kut,,wata kuma?ta daga mata kai,.
Tasleem ta sake matsowa "Kwantar da hankalin ki,ni nasan
Hajiya bama zata soma yadda ba,,Wai mata 2,,kuma kar ki
ji kom,ya Hafeez na son ki,kawai dai miskili ne na karshe,,
ni nasan indai da Hajiya,toh ke kadai ce Matar shi,. Ta
share mata hawaye,.sai lokacin ta dan sararawa kanta..
Shikwa Bayan Abban yace zai ma Hajiyan magana,yai ta
murna,abincin da bai ciba yai daki,,wata zuciyar tace" Toh
kai da kake ta murna, tukun Sa'an ma ka same son ta ne??
sai kuma yai Jim,Toh fa,tanan gizo ke sakar, shifa bai ma
San ya ake cewa a wajen budurwa ba bare in yaje ya tsara
ta taso shi,,yai kamar ya kira Aminu,abokin shi ne ya fado
mishi,wani dan Delhi da sukai school a Hyderabad, ya tuno
yadda yake tsara yan mata,duk mai ji da kanta a school din
tasan da zaman Kunal,.tuni ya kira ya kora mai bayani,,yai
dariya Shima son ran shi, dan jin Wai Hafeez ya fada tarkon
so,,Yace mishi ai ba'a koya zance,sai dai ya dan bashi
wasu formula,.

Read More

== RAYUWAR NIHILA 5 ==

== RAYUWAR NIHILA 5 ==
.
An kai sauran amaren gidajensu Wanda suka sha jere kudi
ya barnatu kam ba laifi saidai fatan alkhairi.. Nihila kuwa
duk ta rame ta zama so silent kullun tana addua Allah ya
jikan mijinta yakai haske kabarin sa.. ranan baban ta yaga
duk ta zama wani iri saiya shirya musu fita picnic dan ta
Dan samu walwala sunyi inviting hardasu beejay da sausan
da mazajen su sukaje lake view Ana zaune Ana Dan ciye
ciye kawai sai baban nihila ya tashi daga ganin wani
mutumi shima mutumin daga ganin shi ta zo wurin da
fiskan mamaki yace jameel kana rayuwan nan ashe zamu
kara haduwa its been ages frnd yace hmm kaidai bari
Muhammad feels good to see old faces again yaranka
nawa yanzu yace gasunan family na ku gaisa ya masa
introducing duka yaransa sannan yace kaifa yace shima
tare da family dinsa yazo bari ya kirasu yaje ya taho dasu
tun daga nesa nihika keji gabanta na fadi wani abu ke yawo
a ranta aikuwaa suna matsowa wa zata gani inba hisham
ba hisham kuwa ji yayi kanshi na sarawa wani flashes yake
gani a idonshi nan ya fadi sumamme aiko nihila da gudu ta
tashi bata ma san tayi ba tana kuka tana girgiza hisham pls
dnt leave me hisham Dan Allah ka tashi I can't live without
u. iyaye dai abu ya kulle musu kai Dan haka kowa da
tambaya fal a ransa amma dai akayi asibiti Dan ceto ran
hisham koma meye ayi bayan nan!!!!
.
Nan dai suka garzaya sai asibiti doctors suka shige dashi
ciki sun fito suke cewa yayi regaining memory dinshi za'a
iya ganin shi inya tashi daga bacci suna shiga dakin ya fara
motsi bude idon da zaiyi ya fara da nihila ta matso kusa da
gadon akace gatanan nan dai iyayen sa suka yi hamdala..
ranan a gidansu nihila aka taru Dan jin bakin kowa nan ne
suke gaya ma iyayen nasu ai sune wanda suke fada musu
tun da can da suke cewa bazai yiwu ba su auri juna baban
nihila yace kaji jameelu Allah mai iko ba yanda baya abunsa
ashe Dan gida nema ni ban sani baban hisham yace ai Allah
ba ta yanda baya abunsa in dai ya rubuta zai faru magana
ta kare.
.
HISHAM ne tambayan daddyn yanda yasan baban nihila
yace mishi tare suka tashi neighbors ne tun suna yara kuma
abokai makaranta daya sukaje tafiyan shi university ya
dawo ya samu muhammad bayanan da en gidan su wai sun
kaura sun bar garin kuma ba wanda ya barwa sallahun inda
suka kaura yaji ba dadi Dan sun saba sosai tun yarinta tare
suke komai farat daya ya neme shi ya rasa sai gashi su
zasu hadasu suke neman hana alkhairi amma da ke Allah
yayi gashi sun hadu da juna. sai musan yanda za'ayi kan
maganan yarannan a turo manya ayi magana tunda dama
suna son junansu baban nihila ya basu labarin auren da tayi
hisham har yaji wani abu ya tokare shi ya zaci an Dan dana
amaryar sa nima na Dan dara aka ce masa ai ran auren
Allah ya dau ran abunsa ya ji sa'ida a ransa Saura sati
daurin auren nihila da hisham sai shirye shirye suke kowa
ransa kal amma nihila ta dau alwashin saita yi maganin
gogan ladan karyan da ya mata yazo gida Dan tambayanta
abunda take bukata taci kwalliyan ta cikin wani lace
turquoise blue mai ratsin pink Ga daurin nan an kafa shi
tasa powder kawai da lip gloss ta fito da Dan gelenta kan ta
iso ma turaren ta yayi sallama ta zauna kujera kusa da shi
gogan naku fa bakin sa yaki rufuwa sai kallo yake ya saki
baki tace da dai ka kulle bakin naga kuda zai fada ya
kwashe da daria yace kaii madam bakida dama aike din kin
tafi mun da hankali tace ahh kai Dan Allah dai yace wallahi
kuwa wai mene ake ta Shan kunu tace hakan nake muradi
yace umm ran gimbiya shi dade ai yanda kikeso haka za'ayi
ta Dan murmusa ta juya ido nan dai suka tattauna kan
abubuwan da zasuyi da kuma abunda zata bukata ya bata
kudi ya tafi.
.
Ranar jumm'a daurin aure nima nace zan gayyaci su
halyma qawata da erta amna er disin sidin bayan ludayi A
yau ne aka daura auren NIHILA Muhammad da HISHAM
jameel bil adama sun taru a wurin kam ba'a magana anyi
reception na gani na fada da dare kuwa dinner aka tafi
tasha kyau sosai ma mutane an hallara a wurin dinner
nagano su marwanatu su phary su maryamah sai hange
suke ko zasu Ga ango da amaryanace inaaa bazan bari a
gansu ba tukunna kowa yana zaune ango ya doso hall rike
da hannun amaryarsa sun balain yin kyau sun kuma dace
da juna hisham baki har kunne sai daukan su picx ake tayi
har suka zauna anyi barnan kudi an ci ansha an hantse
nima dai nace rana daya na mai gayya ne shiyasa na dan
taka rawa aka gama dinner aka watse hisham ne ya Maida
amaryarsa gida suna mota yayi parking yace mata u look
so beautiful my beloved wife kanta na kasa tana wasa da
yatsunta wani sabon kunyan shi takeji ya kama hannayenta
ya rike tayi ta sake amma ta kasa nan ta fara masa
shagwaba yayi hakuri ya barta ta shige ciki yace shi ina
ruwansa shida matar sa ina ruwan wani da kyar dai ya
yarda ya barta ta fita ta shige washe gari aka kai amarya
gombawa diban fari ba'a kwan damu ba an tashi damu
mudin kenan amarya tasha kukan rabuwa da dangin ta
washe gari kowa ya koma inda ya fito daga amarya sai
ango .

Read More

*** *BARIKI IYAWA PART 9* ***

*** *BARIKI IYAWA PART 9* ***
.
Ta kallo fadeela da har ta fara hawaye,, tai murmushi,,sai
da ta dai daici Alhaji zai shigo ta zauna tare da rukunkumo
fadeela,, ta daga murya "Taji ita yar talakwa ce,masu
kwadayin abun Duniya,,Munji mu ya'yan masu da maula
ne,,munji Uban mu baida halin siyan kujera dole ki zage
mu,..da sauri Alhajin ya shigo,," Subhanallah, Sa'a mey ya
faru,,tuni ta tashi,,"yauwa,gwara da kazo,,Yau in kaga na
bar gidan nan toh anyi ta ta kare wlh,,Yace"Sa'a meya faru
ne,,fadeela, me ya faru kike kuka?Sa'a ta kallo Matar
tashi,kan ta nuno ta da hannu, "Matar kace,,samun ta nai a
kanta tana ta Nada,,dake ita kuma doluwa ce ta tsaya ana
dukan ta kamar jaka,, daga rabiya ta dawo kaina,,Wai mu
ya'yan matsiyata,sai fadeela ta bar mata gida,,Dana
tambayi fadeelan sai cewa tayi daga fitowa zata shiga
kitchen ta tare hanya,,Wai ai ba chokalin ta a ciki,,.daga
sake hanya ta hau ta da duka.. Gata nan ta Musa,,tuni ya
hau 90,,yayo kanta zai mare ta ta kauce"Dama na fuskanci
Rabi kullum yarinyar nan rama take,,kwata kwata taki
sakewa da gidan nan,, ina tambaye ta baiwar Allah tace ba
komai,, Ashe gori kike mata harda hadawa da duka?a gida
na? ta kada kai zatai magana tuni ya kara tunxuro,, " karya
na miki kenan??ta girgiza kai,,ya cigaba"kuma da kike kiran
ba chokalin uban ta,ke da na naki uban,, tuni ta kallo Sa'a,
Sa'an ta kanne mata ido daya,,kan ta kallo Alhaji, "ai zance
ya kare,, yau kam zan fadi komai in naje gida,da sauri ya yo
gun Sa'an jiki na bari" aa Qanwata,.kar muyi haka dake,,kar
su dauke ni wanda ban isa da gida na ba,,zan dau mataki
ai,,dole kowa tai hurumin ta,,wlh babu takura a
gidana,,saboda haka Rabi ki kiyaye wlh,,so da kauna yasa
na auro fadeela,,dole tai son ranta a gidan nan da itama
nata ne..ta kallo shi "Toh Alhaji ba komai,,ta kallo Rabin,, "
Aunty ni zan tafi,,Allah kiyaye gaba,ta kallo fadeela da
Alhaji,, "na wuce,dama zan wuce ne na shigo mu gaisa,, ya
wage baki" Atoh toh kin kyauta,,ya zaro kudi a aljihun
shi,,"gashi Haj Sa'a asha mai,,ta kada kai "Alhaji harda
wahala?
.
Ta dan Durkusa" toh na gode,,Yace"mu rakata man fadeela
koh?ta kada kai ya matso ba ko kunya yana goge mata ido,,
Sa'a tai wani murmushin, kai da gani kasan na mugunta
ne,ta kallo Haj Rabi,,tare da daga mata gira,,ta zuge jaka ta
dakko wani katon glass su Alhaji sukai waje,tana kokarin
sawa tace"Yato kika ga??ta dau jakar ta tai hanyar waje"ki
gode Allah da yau banyi wanda zaki yi gida ba,,. Ta daga
mata yatsu 2, "sai gani na 2,wlh ki gyara koh na gyara
ki,..tai waje..Wai Saida ta fita tai yunkurin sha kota,sai sai
kan ta kai kofa har ta fice,ba abin ta bita ba Alhaji na
waje,..Sai yanxu taji hawaye na zubo mata,, lalle Alhaji,
wato sirrin ta karafkaf ya kwasa ya kaiwa dangin amaryar
sa..? Bayan Sunyi sallama da Alhaji ta kallo ta,zan kira
ki,yanxu kibi mijin ki,,saura ki tsaya wannan Dolan cin
naki.. Ta bude kofa ta fita,,fadeela ta bita da murmushi, dan
uwa mai dadi,,Allah yaga tana son mijin ta,duk da badan
Allah bai bashi haihuwa ba da yana da kusan kamar ta.. Ta
kada kai, Ashe hakane abun,.kuka ta samu Haj Rabi nayi
reras,dan Alhaji yace in fadeela ta shigo ta bata hakurin
dukan da ta mata..Wai Alhaji yai mata wulakanci DAN bata
haihu ba..
.
Yace" ke kika ce haka bani ba,abu 1 ne bazan dauka ba,,tuni
fadeela tai ciki,.chan Shima yabi bayan ta ya barta parlour
tana ta rasgar kuka,,gashi ba wanda take sakar wa a dangin
mijin hatta Hajiyan shi ba dadin ta take ji ba bare ta kai
kara. 5:08 tana gidan Ummi,, da gudu ummin ta rukunkume
ta har suna shirin faduwa,, kan ta dago tare da ture ta
kujera,,"Dallah na manta ma munyi fada,, wlh baki m Sa'a,,
ta marai rai ce "yi hakuri, tace" na zata ko lefin ya shafe mu
ne na ran dinner? Tai murmushi, "bar tuna min,ya wuce
ai,.da mamaki ta kallo ta,, ta tashi,meye yake kamshi
haka?kai shegiyar qawa,,ke ai bana shakkun ki,,ba kamar
waccan ba,,tai daki," Wai ina angon ne?ta biyo ta, "yanxu
zaki gansu,.tace" inye, qawata komai yaji,Allah sanya
alkairi, sannan a dage, yanxu BARIKI zatai aiki..
.
suka tafa..sun koma parlour taji wayan ta na kuka,, ta
dauka,fadeela ce,."ya akai auntyn tsoro? Tai murmushi, kai
wlh Sa'a baki da kyau,tai murmushi kan tace"kwarai
kuwa,ko nai wanka ba..tace"ke kinga yadda yazo yana
lallaba ta,harda Durkusawa fa a kasa, Wai shiga in kara
baki hakuri kar ki fada a gida,,tai kwafa"ai kinga illar
nunawa kishiya tsoron ta,, fir ke kenan kullum akaje gidan
ki kina daki,,bazaki ware ki kama mijin ki ba,, bari kiji,idan
har zakina tuna wa da wata a gida bazaki Iya komai ba a
gidan Miji,,tukun ina kayan nan Dana kawo miki? tace"suna
nan,"da fatan kina amfani da su?ta kada kai, gaskiya ban
fara ba..ta kada kai "Toh in kin fara mayi maganar,,.dai dai
nan taji hayaniyar su Aminu,,lokacin tana fadin "nidai ina
fada miki kishiya ba abar tsoro bace,atoh u better wake up
n shine ur eyes,,.ta tsaya da magana ganin da wanda
Aminu ya shigo,.tace" bari inna je gida zan kira ki,da kallo
itama ta bishi,,yayi kyau cikin kana nan kaya,,sai murmushi
yake sakar wa,,fuskar ta ba yabo ba fallasa,,Aminu yace
"Kaga Alalar Geto,, wato BARIKI.. IYAWA,, tuni fara'ar fuskar
Hafeez ta kau.. Maimakon ta kalli Aminun sai ta ke kallon
Hafeez din.
,
Ta maida kallon ta kan Aminu,"Ango kasha kamshi,,ya Dan
bata rai,"au,ai munyi fushi ma Ashe,tai murmushi ta dan
sachi kallon Hafeez din,, duk yai kicin kicin,,tace "ai hakuri
dai,gani nazo,,ya kalli Hafeez, ya sake kallon Sa'a,, yai
murmushi, halin su sai su..tashi yai yabi Matar shi daki..
.
Ya bar kallon wayar ya kallo ta,.duk ranshi ba dadi, suka
hada ido yai mata kirrr,,tana ganin haka itama ta cinkune
fuska,.sun dan jima ba wanda Yace da wani uffan,, chan
dai ya nisa,," Amma kin San BARIKI ba sunan azziki bane
ba koh Sa'a?? Ta kallo shi da mamaki,,baki sake.,yaci
gaba,,"Gaskiya Lamarin duk bai dace da ke ba..ta dallah
mishi harara,.kaga karfin hali,Wai Barawo da
sallama,."Toh,Abba na,,"meye ruwan ka da Lamari na toh??
ganin ta fara daukar zafi yasa ya sakko.. "No,
Sa'adatu,,BARIKIN ne ban son ana fada miki,ina tsananin jin
zafi,..da sauri ta daga mishi hannu.,"Zafi?sai ta zata ko
wani fadan yake nema..cikin fada tace"Ni dauka ta My
professional life was my personal life,,ta hade girar sama
da kasa..da lumana ta karasa fadin" stay out of it..ok?.ta
fara kun kuni a hankali"kaji min mutum da karfin hali..ta
daura kafa 1 kan 1,,yai murmushi,,"Allah ya huci zuciyar ki
yan mata,," my mistake.. Tun daga lokacin bai sake ce
mata komai ba ya dukufa a wayan shi,,ta dan kallo shi, jin
yai shiru,,kanshi kasa,ta dan harare shi,.kan ta
cigaba..lokaci lokaci tana dan Harar shi,kamar wanda laifin
shi ke karuwa..Text taji ya shigo,,tai kamar karta bude tana
chat..
.
Ta dai sauka,.abinda ta gani yasa ta kalle shi,,wai "Meye
kike harara ta??ta murguda baki..taki reply..Chan wani text
din ya shigo, " mey kuma nai na murguda baki??..ta kallo
shi da niyar tace "anyi din,sai kawai taga Shima ya murguda
mata baki,,bata san lokacin da murmushi ya subuce mata
ba,,harda dan dariya mai sauti..ya kallo ta yana
murmushi,.haka suke kallon juna da murmushi, har ta
manta da komai,,tunda take,bata taba kallon Hafeez ba irin
na yau,, Hadadden saurayi ne mai barazanar zama
tunxuru,fari ne,ba chan ba,yana da saje, mai taken Razana
mata,, kyawun shi na Fulani biyu,yana da kwarjini a
fuska,,da dan gashi wajen gemun shi zuwa sage,anyi aski
sai yai mishi dan dass.. Murmushin shi yafi komai tafiya da
hankalin mata,dan baiyanar kyawawan farin hakwaran shi
Tass dasu,,dogo ne,Amma ba chan ba,sannan yana da
kaurin jiki,a dire yake,. Uhmmmm"Aminu ne yai murmushi,,
da sauri ta saukar da kanta kasa cike da jin haushin
kanta.,Hafeez ya harari Aminu,, shikwa murmushi yai tare
da kada kai,. Da halamun hasashen shi ya kusa zama
gaskiya.

Read More

LABARAI DA DUMI DUMINSU

Bayanai da dumi-duminsu na ce wa an ceto turawan Jamus
din nan guda biyu da aka yi garkuwa da su a yankin Kagarko
da ke jihar Kaduna.
A ranar Laraba ne dai rundunar 'yan sandan jihar ta
tabbatar da yin garkuwa da Farfesa Peter Breunig da
Johannes Buringer wadanda suka kwashe fiye da shekara
goma suna nazari kan kayan tarihin al'ummar NOK da ke
yankin.
Su dai mutanen biyu masu nazari ne kan tarihi na
abubuwan da ke binne a karkashin kasa.

Read More

MAGANI DA AIKINSA

MUFATUHATI
1. Game da wadanda suke da matsalar gaba ko kankancewar gaba, karanchin kaurin gaba, ko matan da basa jin dadin jima'i, ko kuma kurajen gaba, ko rashin al'ada, akansha wannan maganin kwana sha biyar(15)
2. Gameda wadanda suke fama da kaikayin jiki ko ciwon jiki, kona gabobi ko fitsarin jini ko fitowar farin ruwa bayan fitsari, ko yawan ciwon kai, asha wannan maganin kwana goma(10)
3. Gameda masu yawan bari(rashin zaman ciki) ko matar da bata haihuwa da kanta, Asha wannan maganin a watan farko da watan uku, da watan bakwai, da watan haihuwa ko wanne wata kwana goma (10)
          TEL:
      08143296981

Read More

****GIRKE-GIRKENMU****


Read More

== RAYUWAR NIHILA 4 ==

== RAYUWAR NIHILA 4 ==
.
Momin hisham ta samu baban shi da batun maganar
hisham yace karma ta fara yasa ta kira hisham yace masa
yama cire rai matan gombe duk sun kare ne da har zaije
abuja neman wata bai yarda ba hisham ya tashi jiki ba laka
ya tafi Dakin sa ya rasa me zaiyi yaji dadi ga nihila is
against him kawai ya tattara kayanshi na sati da duk
abunda zai bukata ya fita iyayen shi basu saniba ya shige
motan sa bai zame ko ina ba sai hanyan Abuja gudu yake
baima ganin gaban shi shi kanshi baisan ina yake dosa ba
kawai saiga wata daf ta doso shi ba birki yana ta mishi
horn amma ina hisham hankalin sa baya jikinsa ji kake
kyarrrrrrrrrr mutane suka yo agaji dan ganin motan basu
zaci mutum zai fito da raiba dama suna kusa da abj kawai
akayi dashi cikin gari.
.
Nihila kuwa tana can abun duniya ya dameta dan kuwa
baban ta ya kawo wani maganan da ta kasa zama a kanta
tsaban girman sa wai zasu kara karfin zumunci da babban
abokin shi Dan haka sun hada yayansu aure shi kuwa nihila
yace ya bada ganin duka sauran sunada samarin su inyaso
sai a hadasu duka at a time.Taci kuka sosai harta gode ma
Allah taso tayi ma babanta maganan tanada wanda take so
amma momin su ya kwabeta karta kuskura taga ma it's of
no use gwara ta hakura ta manta da hisham tayi biyayya
Ga iyayenta.... tana zaune aka zo akace ana neman nihila a
waje tace waye aka ce mata wani da kaman bazata je ba
sai kuma tace bari ta fita ta gani to her suprise wa zata gani
inba jawad mutumin da sukayi kusan shekara basu hadu ba
tun graduation dinsu tayi mamaki kwarai batasan sanda ta
fara daria ba tace jawad kana duniyan nan yace inanan
nuhila ya bayan rabuwa tace lafiya how's your life..
.
Alhamdulillah na dawo skul nace dole inzo in ganki sabida
it's been long tace kaidai jawad bari ta bashi labarin duk
yanda take ciki yace mata nihila kinyi hakuri kiyi biyayya Ga
iyayen ki insha Allah shine alkhairi a rayuwanki tace
shikenan yace shi zai tafi zaizo dubata in ya kara hutawa
sukayi salaam. Hisham kuwa yana can asibiti likitoci suna
kanshi daga karshe dai suka gano yayi loosing memory
dinshi temporarily kuma Ga karaya biyu a kafa.. suka rasa
yanda za'ayi a samu wani nashi sai kawai suka bada
sanarwa a tv da hoton shi da sunan da suka gani jikin wallet
dinshi anata cigiya ko Allah zaisa a gano yan uwanshi...
iyayen hisham kuwa neman duniyan nan sun yi basu ganshi
ba hankali ya tashi sosai ma matuka maman shi har kuka
ta fara ana haka ne aka kirata wata kawarta ta dauka jiki ba
dadi tace ta kunna tv ta na kunnawa saiga sanarwa ana
neman yan uwan wannan bawan Allah mai suna hisham
wanda ya gamu da hatsarin mota kuma yayi loosing
memory dan haka idan yan uwanshi suna kallo su gaggauta
zuwa abuja nan suka ba da address din asibitin ko zaiyi
recognising dinsu ai sai faduwa tayi a wurin baban hankalin
shi ya matukar tashi ta farfado tace Allah fir akama hanya a
tafi a nemo mata danta haka sukayi booking flight washe
gari sukaje Abj basu tsaya no ina ba sai asibitin suka ce
sune iyayenshi aka kaisu har dakin aiko dai hisham bai
ganesu ba yace musu kudin wayene sai maman shi kawai
ta fashe da kuka haka dai likita yayi ta rarrashin ta yace
tayi hakuri irin wannan matsalolin sai a hankali inba mutum
yaga abunda yake tunani last ba ko kuma something very
important in his life nanne in anci sa'a saiya samu
memories dinshi back other wise sai wani ikon Allah.
.
hakadai iyayensa sukayi ta jinya a asibiti har ya farajin
saukin karayan da yayi yana healing amma memory kam
babu... ummm wannan kenan ko yaya amarya NIHILA tayi?
Ga rashin masoyi Ga auran wanda bataso...muje zuwa
Ananan anata shirye shiryen auren su anata gyara amaren..
nihila kuwa ko taba ganin angon nata batayi ba Dan ance
mata baya kasan sai ranan daurin aure zai dawo sunan shi
junaid akazo ranan daurin aure an daura na sausan da
yusuf.. bahijja da anwar sai nihila da junaid.. an daura aure
ana reception ne aka zoma iyayen biki da wani mummunan
sako akan ango nihila sun samu hatsari akan hanyan zuwa
daurin aure inda motansu ta kone kurmus sukayi mutuwan
shahada kowa yaji ba dadi haka aka kwashi jiki akaje aka
kaisu gidan gaskia.. nihila nacan tana shargar kukan ta
batasan meke faruwa ba tana ta inama ace yau da hisham
aka daura mata aure saidai kashh bakin alkalami ya riga ya
bushe.Baban tane ya daure yazo ya sameta yayi ta mata
nasiha mai shiga ciki yace komai yiwuwan ubangiji ne kuma
Allah ba yanda baya abunsa shike bayarwa shike kuma
hanawa a lokacin daya so jikin ta yayi sanyi tasan wani abu
ne ya faru tace daddy ka gayamun ko menene nayi alkawari
zan iya yace mata nihila Allah ya miki albarka biyayyan da
kika mana Allah ya dau ran wanda muka baki sai taji
hawaye a idonta tace Allahu akbar Allahu akbar Allahu
akbar Alhamdulillah ala kulli na dau wannan qaddara hannu
bibbiyu Allah ya musanya mun da mafificin sa uban ya
rungumeta yana kuka tanayi nima na Dan tayasu Dan
tausayi.

Read More

==RAYUWAR NIHILA 3==

==RAYUWAR NIHILA 3== .
Daddy shi ya dawo da maghrib yaje ya sameshi har parlour
uban ya rungumi dansa sukayi musabaha ya gaisheshi
sunata labari saiga mum dinsa tazo tace ooh yanzu alhaji
da yaron nan ne ka zauna sai hira kake kaman wani sa'an
ka yace haba ke kuwa altine in banyi dashi ba dawa zanyi
shi kadai fa nakeda ai dole in soshi.
.
WANE NE HISHAM? Dane daya tilo ga alhaji jameel pindiga
tunda sukayi auren zumunci da altine yar wajen ummansa
ce shekaran su 5 Allah be basu rabo ba ana shida ta samu
ciki ta haifa da namiji aka sa mishi hisham daganan kuma
shiru ba aihuwa ba labarinshi. son dau son duniya Sun
daura mishi primary kawai yayi a nigeria Amma secondary
da university duk a cyprus yayi. Hisham fari ne ba kuma
fari har can ba yanada kiran maza wanda suka amsa sunan
su dan daga nesa zaka hango abs din da Allah ya masa Ga
faffadan jirgi da tsayi he's just the perfect guy da mata ke
so saidai duka wannan kyan Dan maciji ne dan kuwa
zuwansa Cyprus ya lalace da neman mata da zuwa clubs
sa'a daya dai baya shaye Shaye.Hankalin sa tashi yayi da
yaji fadan da daddyn yake tayi akan wani cousin dinshi yaje
neman aure har sokoto yace shi bazai lamunta in bazai
nema auren a gombe ba ko wani wuri kusa bazaije masa ba
sabida nisa da kuma rashin sanin tushe.wani gumi yaji ya
tsatssafo masa ya ji jikin shi ya mutu ya tuno da nihilan sa
Wanda bazai iya rayuwa babu ita ba gashi yanaso yaje ya
ganta Amma babu hali Dan kuwa daddyn shi ya sashi a
gaba da ayyukan company dinsa atm dinsa gaba daya
suna hanun hisham minti daya biyu zai neme shi yace it's
high time ya zama responsible man. nihila kuwa tana can ta
rasa meke mata dadi idan taga pictures din hisham da
emmata a wayanta saitaji duk ya fara bata haushi tace yau
kam ko mutuwa za'ayi sai sunyi ta ta kare.
.
Ta shiga watsapp dinta saita tura picx din Wa hisham yana
zaune yana tunanin yanda zaiyi da daddyn shi batun nihila
kawai yaga watsapp dinshi ta turo picx baisan sanda ya
tashi tsaye yana zaro ido ba hankalin sa ya balain tashi
tambaya kala kala a ransa ina nihila ta samu pics dinnan
kardai tasan halayen shi wanda yaketa boye mata? Ta ina
zai fara mata bayani gaba daya ya Burkice aiko ana haka
sai ga text dinta hisham ka bani mamaki u disappointed me
I trusted u my whole life Amma da abunda zaka sakamun
kenan? Forget u ever know me in your life. Gud bye. Tashin
hankaliiii!! Ba'a sa maka rana shin kuna ganin hisham zai
hakura kuwa muje zuwa.
.
Hankalin sa a tashe ya kira ta a waya taki dauka missed call
kusan goma sannan ta dauka ana sha dayan tana dauka ya
fara magiya nihila plsss let me explain to you tace ba
abunda zaka gayamun hisham na riga na gani da idona ko
zakace ba kai bane yace nine nihila Amma Dan Allah kiyi
hakuri na miki explaining tace bana bukatan wani
explanation kaban mamaki hisham ashe dama abunda
kakeyi kenan Allah daya halicce ka bakaji tsoron saba mishi
ba baka kuma ji kunyan yana kallon ka saini mutum wanda
ba komai ba baiwar sa ya halicce ni nine zakajin kunyan
idona kar na sani. yace nihila nasan nayi abubuwa da dama
a rayuwa na but wallahi shigowanki rayuwana is a blessing
to me kinsa na daina 70% din abunda nake I have changed
much more than before for u tace ooh sabida nine ma kayi
changing not because kana tsoron abunda zakaje ka tarar
wurin ubangijin ka yayi shuru yana jinta kawai sai hawaye
yaji a idonshi nihila pls dnt leave me without u my life will
be miserable plss nihila tace hisham its too late to cry when
the head has been cut off just leave me alone i adore and
cherish every moment we had together but this has to end
ta fashe da kuka tace goodbye hisham ta kashe wayanta
ma gaba daya tasa favourite waqanta wanda take sawa in
tana bakin ciki wato bhula dena (forget me) na ashiqui ta
kuka har taji ba dadi.Taci kukanta son ranta saiga bahijja ta
tsaya tana tausaya mata duk tasan be wuce kan hisham ba
ta girgiza kai sis meya sameki kawai ta qara fashewa da
kuka ta rungumi beejay he betrayed my trust and life beejay
he lied to me ya zanyi da raina gashi mummy tace na fita
harkanshi bata yarda da soyayyan mu ba i just dont know
what to do beejay ta rarrasheta tace mata tayi hakuri ta
manta da hisham sabida koda ya canja halin sa iyayen su
da kyar ne su yarda sabida nisan garuruwan da suke kuma
basa son auren nesa. idonta duk sun kumbura sunyi ja ta
dawo kaman ba lively nihilan da take da ba ta canja
completely.
.
Hisham kuwa yana kuka ya je ya samu mum dinshi tace
hisham lafiya me haka kake kuka kaman yaro wa nine ya
mutu yace momi aa ba mutuwa bane wata yarinya ce ya
bata labarin nihila amma bai gaya mata dalilin fadan ba
kasancewar suma iyayen basusan tsiyar da yake tafkawa
ba Dan inya dawo nutsuwa yake tace hisham da ka hakura
da yarinyar kasan daddyn ka ba yarda zaiyi ba da kunnen
ka kaji yana fada akan neman auren da cousin dinka yaje
yi a sokoto bazai bari ba yace mommy wlh bazan iyaba kiyi
hakuri ki mishi magana she's my life tace shikenan zan
gwada amma abunda kamar wuya.

Read More

== RAYUWAR NIHILA 2 ==


== RAYUWAR NIHILA 2 ==
.
Na tsaya kawai ina sake da baki nace beejay yanzu kin
kyauta ma kanki kenan kiji tsoron Allah fa inni na rufa miki
wani ya ganki yaje ya fada fa a gida tace kin fara ko naji
shikenan a haka dai ta gama rawe rawen ta suka koma gida
nihila na jimamun alamari irin na bahijja.Sun koma gida
beejay ta Kara tunatar da ita batun alkwarin rufe sirri tace
da ita tayi shuru tace toh.. wannan kenan! Suna waya ne da
hisham yake kara tunatar da ita irin sonta da yake nihila kin
sauya mun rayuwa kin canja ni gaba daya wasu abubuwan
da nake da yanzu kusan duk na bari tace wasu irin
abubuwa yace hmm bazaki gane ba sai a hankali nidai pls
keep my love I promise I will be the best u ever had n I will
make u my wife! Ummm hisham kenan...
.
Yana can yana tsula tsiyar shi son ranshi a kasar cyprus
wanda shi a ganin shi wayewa ne ya kawo hakan Ga neman
mata ga zuwa clubs kowace rana saiya yi attending ba'a
barin shi a baya shima wai bazai bawa shedan kunya ba...
nihila tace yau kam bari ta shiga account din hisham na
insta tayi bincike tana shiga taga pictures kusan 30 ta shiga
ta fara duba comments duk wani abokin shi da taga yayi
comment shima sai ta shiga account dinsa ta duba hmmm
me zata gani saiga pictures din hisham baja Baja da
emmata a clubs ya kamo wannan ya kamo wancan ta ji
kaman an caka mata wani abu a zuciyanta..
.
Nima daganan saida naji rasssss.. batasan sanda hawaye
ya zubo mata a idonta ba tayi munching picx din duk ta
ajiye.. comments din mata kam kala kala kan pics dinshi
daga wnda yake cema sweetheart sai me my wife da dai
sauransu ta ajiye wayanta ta rasa meke mata dadi tasaka
waqar bhula dena(forget me) na ashiqui ta risgi kuka son
ranta saida idonta sukayi luhu luhu har bacci ya dauketa
anan sausan tazo ta sameta ta dau wayanta ta bude kawai
saitaga picx aiko ta tura taje ta nuna ma momin su waiga
samarin da nihila take so en iska marasa tarbiyya... Ran
momin su da yayi dubu saida ya baci ta sameta a daki ta
mata tas tace tunda taki jin maganan ta bazata bada wayan
ba sai taga canji a tattare da ita..
.
Tayi kuka sosai da taje skul take gaya ma habibaty tayi ta
bata hakuri sannan tace mata itama ta hakura da hisham
din mana tace mata inaa bazata iya ba tasan hisham yana
sonta ita kuma ta dau alkawarin she will change him for
good koda bazata aure shi ba amma bazata barshi a
munanan halayen da yake ba na sabon Ubangiji habibaty
tace shikenan Allah ya baki sa'a... watan ta kusan daya ba
waya har sun gama exams dinsu sannan da kyar da rokon
beejay momi ta bata wayanta hisham kuwa hankalin shi
dayayi dubu saida ya tashi da bai saba jin wayanta a kashe
ba kullun suna waya ko chatting sai yayi tunanin kodai taji
labarin halayen sa shiyasa ta guje shi tanata jimamin abun
a zuciyar shi.. kawai saiga call dinta ya shigo ya dauka
yace haba sweet ina kika shiga for weeks inata nemanki
saita mishi karya tace ai wayanta ne ya fadi saida ta siya
sabo yace kaii har kinsa naji sanyi a raina plss kina sanar
dani irin haka tace to shikenan insha Allah bazata kara ba..
.
Yace yauwa my nihila dats y i love u more n more each day
tace I love you most.. A zuciyanta tana mamaki halin
hisham kaman bashi ta gani da emmata ba abun ma har ta
kasa yarda duk da ta gani da idonta... tace a ranta akwai
ranan tonan asirinka!.Sun gama exams dinsu lafiya aka
fara shirye shiryen candy dinsu murna a wurinsu ba'a
magana dan a kansu ne za'a fara graduation ceremony...
ranan candy sunsha kyau ita da bestyn ta habibaty sunyi
shigen white and black Ga gown dinsu royal blue da white
ya karbesu sosai aka fara gabatarwa inda aka kira Nihila
Muhammad Tahir tazo ta bada opening speech ta fito da
takunta na kasaita kaman gimbiya taje ta bada kaman wata
baturiya nan aka dau tafi raf raf raf sai shewa ake an bada
prizes da dama wanda kusan rabi ita ta dauka tayi kukan
farin ciki bayan taro sun dau pictures sosai da jawad ganin
karshen zaman su yazo yanzu sun bude wani chapter a life
dinsu sunyi kukan rabuwa da jona sabida shi zai tafi
university of
Read More

*** *BARIKI IYAWA PART 7* ***


*** *BARIKI IYAWA PART 7* ***
.
Lalle Sa'a, yarsu tana daga cikin wayan da suka zo Duniya
cikin Sa'a,, fatan shi Allah ya cigaba da kare mishi
Sa'adatun shi..Lalle kam taci sunan masu sunan nata
"SA'ADATU SA'AR MATA..(na Damary en Feenat)..
Washegari gidan su Ummi aka fara sauka,, dan tunda ta sa
rai da mota tai joining class inda ake training, cikin 4 days
kwa ta Iya mota,,da mamakin ta data shiga taji tana zugar
ta..." Wayyo dadi..da gudu ta shiga gidan su Ummi, ba ko
sallama "Qawata...Ummi.,woo fito kisha kallo..ta fito daga
kitchen da mamakin sammakon Sa'a yau,,,dan sai 9 suke
da lectures,,suka ci karo" Sa'a,. Lfy?maman Ummin ma ta
fito,,jin sun wani kwalla musu ihu a cikin gida.."Lfyn Ku
kuwa yaran?ina ai har sunyi waje,.ta girgiza kai "Allah ka
shiryi Sa'a da Ummi,.. Tai kitchen dan duba abinda Ummin
ta bari a wuta..da karadi suka shigo gidan"kai shegiyar
gari.
.
kin Faso mu da yawa,yau dole mu tada kura a schl.. "Duk
dan uban da bai tayamu celebration ba bamu bashi,..suka
kyalkyala dariya., mama ta fito,," zanga ranar da zakuyi
hankali yaran nan.. Suka kallo ta,kan ta gaida ta, tace"oh
Wai murnar ta meye wannan? Da sauri Ummi tace"Mama
mota fa mukai?wanda zai aure ta senator nan ne ya siya
mata..da sauri Sa'a ta kallo ta, sai ta kanne mata ido, "tace
mama karya take wlh,,ni saboda Allah ya ban dan na mishi
campaign din partn su..ta kallo Ummi, " kullum sai na ce
miki ban son karya,,ta kalli mama"mama nasan kin yarda
dani tamkar wacce ta Haifa ko? Maman ta kada kai, ta kallo
Ummi tare da Harar ta"ni zuba mana abinci in kin gama,,ta
kalli mama tare da mata murmushi.. Sukai kitchen. Tuni
karya ta karu wajen Sa'a,, ansa bikin fadeela itama,,tuni
suka hau shirye shiryen biki,.za'a ai nata kan nasu Ummi,,
Ranar ta fito a gida, tabi layin su Aminu a kafa sukaci karo
dashi,,da abokin shi,, tuni ta hade rai, Shima yana ganin ta
ya hade rai yaja ya tsaya,,tai mai wani kallo kan ta dawo
kan Aminu, "angon mu,,ya akai? Yai murmushi bayan ya
kare musu kallo duka,," lfy lau,, yau ina motar na ganki a
kasa?ta yatsine fuska,, tana chan gidan da ake ajiye ta,, Da
sauri Hafeez ya kallo su,ta maka mishi harara tare da
kawar da kai.. Duk yana kallon su Aminu.. Hafeez yai dan
tsaki,,"malam kazo mu wuce ni,,ta tabe baki "ai ni ban
tsayar da wani ba anan., ta murguda baki ba tare da ta
kalle shi ba,,ya kalli layin yaga ba jama'a kan ya dawo
kanta" dallah rufen baki a wajen,,ke har kin kai ki tsayar ni
da?.tuni ta kankance ido ta nuno shi da hannu "kar ka kara
ce min dallah chan..ya zaburo kamar mai jira," ance dallah
din,,mey zakiyi?ta matso itama"kaima Dallah chan
toh,,Aminu mai zai inba dariya ba,,Bai san mey yasa jinin su
bai hadu da juna ba,tun haduwar su ta farko,,kuma yasan
duk din su ba masu son fada da jama'a bane.
.
"sarkin yan tusa kai a mutum, ban damu da kai ba ka bi ka
damu dani,yai murmushi "ke a fada miki tusa kai,, macen
da tsabar rashin kamun kanta ba wanda bai Santa ba,,da
sauri ta kallo shi,zata tanka Aminu ya shiga tsakanin su,,"
Wai Ku hala kuna ganin hanjin juna koh??taja baya,, "kaci
Sa'a wlh yau Dana fada maka wacce har ka mutu bazaka
manta ni ba.. Taja tsaki tare da daga wa Aminu yatsun ta ta
wuce,,tuni ya cije lebe tare da rintse ido,, ya bala'in tsanar
tsaki,,kan ya bude ido har tai nisa,," amma ya kamata
kasan ba abu mey kyau kuke ba,,ache kullum kuka hadu sai
kun bar abun fadi?kwanaki naji mey ya faru a super market
ai a wajen Ummi,,na rasa mey ke damun ka kwana 2
nan..ya kallo shi,shi kanshi bazai ce mey ke samun shi ba,,
shida maganar bakin shi ma gagarar shi take,,amma ya
rasa indai suka hadu da Sa'a in basui ba baya ma jin dadi..
Haka akai bikin fadeela sukuku da ita,, idan ta tuno
kalaman Hafeez,, ta tsani a sha da ita a rayuwa, gashi bata
rama ba yazo abu na damun ta.. Sun samu hutun
makaranta a dai dai lokaci,dan yau suka fara shirin
biki,ranar Aminu yazo Yace suzo suje rakasu zabar kayan
taron,ta tambayo mama suka fito,,da ganin Hafeez tace ta
fasa zuwa,,Ummi ta kallo Aminu,, da sauri ya fito,,"kar ki
mana haka Sa'a pls,,kin
Read More

*** *BARIKI IYAWA PART 5* ***


*** *BARIKI IYAWA PART 5* ***
.
Sai bayan la'asar Alhaji ya koma gida,,yasan da zuwan
Matan shi zuwa gidan su BARIKI a bakin Bala driver,, sai dai
da mamakin shi da ya shigo gidan An hadu da yara ana
kallon Namamajo ana ta cin dariya,,kowacce taci Ado,tunda
yake,abinda bai taba gani ba kenan a gidan shi anyi,,Wai a
hadu,uwar gida da ya'yan ta da amarya da Ya'yan ta a waje
daya..tab lalle ya fara ganin sauyi,,dan Babban burin shi
dama Matan su hada kai, ya samu ya'yan shi ma su
hada,,amma ina,ya kasa tsawan shekara 6,.sai gashi a
abinda baifi kwana 3 ba BARIKI ta fara saita gidan shi,,toh
ita kwa mey ta fada musu haka?da wani harshe tai musu
magana wanda shi baiyi ba?? Ya kada kai yai sallama,, da
fara'a suka amsa yaran suka taho da gudu mishi sannu da
zuwa,tare da karbar kayan hannun shi suka ajiye gaban
iyayen,,.Matan suma suka mai,ya amsa da kyar,,dan dole
ya ga sauyawar su koba yau ba,,yai daki,,amarya ta kallo
Hajiyan,, "mu bishi muji.. Suka ran kaya daki,,yana kokarin
cire babbar Riga suka karaso,.karba sukai dukan su suna
cire mishi,,ya tsaya baki sake yana kallon su,, Uwar gida tai
murmushi," Alhaji muna fa sannu da zuwa,.ya kalle su tukun
ya tabe baki,, "Ku Wai nan campaign kuke ne komai?suka
kalli juna" name Alhj? Yai murmushi "na karna auri Sa'a,,
zasui magana ya tsayar su,, " Ba abunda zai hanani auren
Sa'a in fada muku,.gobe ma za'a kai kayan tambaya.. Da
dariya suka fashe mishi,harda tafawa., tuni ya fara
muzurai,, kadde fa sunyi wa yarinyar mutane wani abu??
suka kallo shi, "Na BARIKI manya,,inji amarya,kai kace
mana tusa mata kanka kake bamu Sani ba? Ashe ma ba
son ka ake ba.. Ya bata rai" inji wa?suka hada baki"BARIKI..
Yai murmushi,,"eh a haka zan aure ta,, indai zata bani farin
ciki a gida na,, ya wuce bandaki ya barsu tsaye,,zama sukai
jiran ya fito.."aha Wai Baku tafi bane?? Suka kalle shi,, uwar
gida tai gyaran murya.. "Alhaji,, ya kallo ta" eheem,.ta gyara
zama"wlh ko ba aure mun gyara zaman mu,, kuma koda
aure baza mu saba ba,,kai hakuri, munsan mun bata ma a
baya,, amma wlh gaba bazai kara faruwa ba,,kallon ta
kawai yake ya harde hannu,,tunda suke.basu taba sanar shi
haka ba,,. Amarya ce ta katse shi,. "Nifa dan Allah nayi,,wlh
kama daina cewa dan zaka auro wata BARIKI.. Ehe,.inma
ka auro ta in baka Sani ba Toh yanxu ka Sani,.uwar gida sai
daga mata hannu take halamar tai shiru,amma ina,dan fa
ita yar gaba gaba ce,, tace" in baka Sani ba ka Sani"MATA
UKU.. GOBARA(Na Mrs Jabo)Ce,,ehe,,gwara ma kai
Hudu,.atoh,. yace "kun gama??uwar gida ta kada kai,"toh
koh aman Wuta ne saina auro Sa'a., tashi tai" Hajiya mu
tafi,,kai kuma Allah ya taimake ka..yace"Amin,, Suna fita
uwar gida tace"Amma kin kwafsa mana fa,,tai kicin
kicin.."Hajiya yi hakuri, wlh haushi ya bani,, kamar muna
ziga shi.. Yana jiyo su ta daki,,.. Da dare ya samu BARIKI..
Sai murna yake,yau kam ta biya shi,,yaga abinda bai taba
gani ba a gidan shi,,tai murmushi,"toh Allah yasa sun gyara
kenan,.yace"Amin,. Amma Sa'a, nifa da gaske nake son ki
fa,, wlh jiya da tunanin ki nai bacci..ta kalle shi tare da yin
fari da ido.."Aiya Alhaji,, ina da tsayayye, sai dai baya kasar
nan,PHDn shi in ya dawo muna da alkawarin aure..yai
murmushi "anya Sa'a? Ya kada kai" Any way,, yanxu dai
bamu tsadan ce ba..nawa kike ga zan baki?ta rausayar da
ido,, "Alhaji masu gari,,Ashe ana cini ki kuma daku?yai
murmushi, itama tai,..su BARIKI anso yaudara,,, tace" Ai
zamanin siyasar yanxu da abunda ke hannun Ku manya
ake kyauta ba cini ki ba.. Yanxu muna da kamar Ku a
centern nan amma Bariki bata ko motar hawa..bare na
samu ta raly..ta kanne mai ido 1..tuni ya hau washe baki,,
lalle BARIKI,harda ke a yan campaign din namu Ashe??tace
"kai,sosai, ai partn mu daya..tuni ta hau tsara shi tana kara
kwadaita mishi kujerar da yake nema ta senator.. Dan dadi
bai San ya mata alkawarin mota ba indai ya hau mulki..
Kamar gaske ta kallo shi da mamaki baki sake.." Alhj daga
wasa??yai murmushi.."karki damu.,ai irin ku muke
nema,,bare gaki da mutane,.indai kuka mana campaign yan
partn mu suk
Read More

*** *BARIKI IYAWA PART 4* ***


*** *BARIKI IYAWA PART 4* ***
.
Bai dawo ba sai kusan Tara na dare,tuni suka kara kulewa,,
yana shiga ya gansu zaune a kujera 1 suna ta huci,,ba
wanda yai wa magana yai dakin shi,,da sauri suka tsayar
shi, Wai Alhj mai kake nufi?yaci mur, "danayi mey? "Kazo ka
wuce ba ko magana, yace" ita sallamar ba magana bace?ko
kun amsa?sukai shiru,yace"Ku bani waje..amaryar ta kara
tare kofa"ai wlh sai ka fada mana wace Sa'a a gun ka da
har ta fara shiga lamarin dangin ku,,yai mata wani kallo,,
"Sa'a kuke son Sani? Ta kada kai tare da Rike kugu,,yai
murmushi" itace wacce tasan na Gaji a barni na huta,,ita ke
maraba daku a matsayin kishiyoyin ta da zata samu,,Sa'a,
ta wuce tunanin ki a waje na,,ta tabe baki,, "wannan kai
kasani, abu daya muka Sani, mudin Zaka auro wannan yar
BARIKIN, toh fa tafiya zamuyi,, koh Hajiya? Ita dai uwar
gida tsabar takaici ta kasa cewa komai,,yai murmushi, "
zaku Iya yin komai, amma Sa'a kamar ta shigo ta
gama,,Hajiyan ta tare shi"Alhj bafa zan zauna da Wannan
kilakin ba wlh,,saboda tsabar wulakanci, Wai ita zaka fifita
akan mu tun yanxu? Ya harde hannu"da akai mey?tai mai
banza,,ya gyada kai kan yai daki,,amarya ta kallo uwar
gida,,"Hajiya. Gidan su kawai zamu mu kaddamar mata,, ki
duba tun yanxu mun zama bola?ta kada kai, "Allah ya
kaimu,,. Washegari yana fita suna fita,direct gidan su Sa'a
sukace driver ya kaisu,.zai musu suka hayaiyako mai,, tuni
jiki na bari ya kaisu,,Suka karewa gidan kallo,nanne Wai
gidan su ma,,ciki sukai,lokacin tana brush a gindin famfo,,
da doguwar Riga ta bacci mai silik,da Maman ta suka fara
cin karo,,da mamaki take kallon su, ganin ko sallama sun
shigo gidan,,amaryar ce mai karfin halin tambayar "BARIKI
fa??ta kuskure baki ta juyo rai hade,, suna hada ido suka ga
ta bala'in yi musu kwarjini,,a jinin ta yake,,mudin kaso mata
wulakanci indai kuka hada ido, toh sai dai ita ta sauke
maka,Allah yai mata baiwar Kwarjini... da niyar nadar ta
suka zo ko su ci mutuncin ta,,suka sau baki kallon ta,, mace
kira kamar ita tai kanta?ji uban gashi da fagon wani guri?
hmm lalle kam Sa'a ta wuce tunanin su,,tuni ta wayan ce
wa tayi,tuni ta sau fuska lokacin da ta gane ko su waye
su,,ta ajiye cup din tana kade brush tare da daukar mouth
wash din,," Sannun Ku da zuwa Aunty,..Hajiyan ta kalli
amarya, amarya ta kalli Hajiya.. Hee hee... BARIKI Ake fada
muku,,IYAWA,, ta kallo mama,."ina taburmar nan?baki sake
ta nuna mata kitchen,, ta tafi tana girgiza jiki,da kallo suma
suka bita..ta dakko ta shimfida musu,,ta kallo su da
murmushi,, "ya Ku zauna man,,tamkar wasu masu bin
umarnin ta suka dawo,, ta koma daki ta sako hijab,.ta
zauna," ina kwanan Ku Aunty?a ciki suka amsa,badan sun
so ba,,Ta kallo Maman nata,"mama, baki nane fa,,Matan
Alhj Muktar mai naci Dana ke baki lbr...Ba suba,hatta
maman tata baki sake take kalle ta da sauri,, sukwa tuni
suka gyara zama tare da sakar fuska,, tana ganin haka ta
kada kai da murmushin mugun ta,, a ranta tana "woo ni
BARIKI.
.
Sai lokacin suka gaida Maman,.da mamakin su itama ta
amsa,,ikon Allah, da ganin Matan da rashin mutunci suka
zo gidan,,amma dubi Sa'a cikin seconds da bai wuce 3 ba
har ta shasu,,kai,al'amarin yarinyar nan ita kanta tsoro yake
bata,,Hausa sunce Wai Barewa bata gudu danta yai
rarrafe,,toh gaskiya a kanta ta Musa,,dan ta ko'ina halin ta
bai kama da na Sa'a ba,,da de fadeela ce,,sai dai in ta tuno
ance kowacce mace da irin tata kissar a ake haifar ta,,. Kai
ta kada musu,,ta kallo Maman,,tai mata halamar ta dan
basu waje,,ta gyada kai, "ni zan fita ma,zan leka gidan
gaisuwar nan da baban Ku yaje dazun,, ta kada" sai kin
dawo,, ganan abincin ki a flaks,fadeela tayi makaranta.
.
Ta dawo gun su,"sai anjiman Ku, Ku gaida gida,,suka washe
baki,"a dawo lfy,,Kanta fita Sa'a ta tashi ta dakko musu
drinks a fridge din tsakar gidan,,da cups, ta zauna,,"Bissmil
lahn Ku fa,.suka kalle ta., "anya kuwa,sanyi da safe,tai
murmushi,"toh ya akai? nasan da magana a bakin Ku,,
sukai shiru,,tai murmushi,,zama ta gyara kamar mai
Tahiya,ta dafa kafafun su,," am Aunty,, bari
Read More

*** *BARIKI IYAWA PART 3* ***


*** *BARIKI IYAWA PART 3* ***
.
Ya danna kira ya sanar ta ya akai,"ka barta zuwa gobe da
safe,,nasan zata ce zata zo wuri na,,ko tasa azo,, kai mata
gargadin wannan kan ka fita,,. Washegari ma bai sauya
ba,yau Aisha harda su gaisuwa, wanda rabon ta da yi tun
Kan ta sauya hali,, yai mata banza,,zai fita cikin sanyi tace
baka karya ba,,ya harari wajen abincin, "No zan karya a
waje,,sannan ban yarda ki daga daga nan ba,zan Iya dawo
wa kowanne lokaci..
.
Yai waje yana dariyar keta,,a kujera ta zube,,tunda take
Abban Najib bai taba mata haka ba,,Wai har abinci bazai ci
ba.,ta share hawaye,Kila ma wajen BARIKI zai ciwo,,kai
amma su salma sun mata huduba marar kyau,, gashi ta
kwabe mata,, waya ta dauka,kan ta kira salman," karki
zomin gida,munafukai kawai,,kit ta kashe wayar ta,, yanxu
ta ina zata fara? Acikin kwana 2 duk ya sauya mata
hali,Waya da BARIKI, text kuwa ba'a magana, ranar yana
wanka ta saci numbern bariki a wayan shi,da sauri ta
fita,,sai sa ya yay kan ta kira BARIKI,, a yangance ta dauka,,
"Amm Aisha ce,,tai far " wacce kenan? Duk ta rasa abun
fadi, dan ji tai ta mata kwarjini tun a waya..sai kawai ta
kashe,,.bashi ya dawo ba sai azahar,, kuka ya same ta
tanayi reras,, tana ganin shi ta tashi,, dan dazun nan aka
kara karanta mata wace BARIKI yar unguwar su,,"Baban
Najib,,dan Allah ka auri kowa banda sa'a,, kayi hakuri bazan
kara ba,, ya kallo ta kamar yai dariya.,a ranshi yana tunanin
"Wai meye da BARIKI ne da yasa mata ke tsoron ta?? Ya
basar" Gaskiya bazan Iya fasa auren Sa'a ba,, dan tun
yanxu tai min alkawarin zaman lfy da kwanciyar hankali,,
bazan fasa ki koma min yar gidan jiya ba.., tuni ta hau
rantsuwa ta daina,inta kuma ya auri BARIKI,, da wannan ya
samu lfy a gidan shi,,yace da yamma muje zan raka ka.
.
Yamma nayi suka je gidan su BARIKI,, a lokacin tana gida
ana drama da ita,,wani kanin kakan su yazo daga
Nguru,amma irin in za'a bi da aure tsakani,, yazo akan lalle
lalle BARIKI ta fidda Miji,,tunda fadeela ta fitar,,tuni ta
fitsare "Ni fa banni da tsayayye,, atoh ko ina da wallahi ba
zanyi aure yanxu ba,,baki ya saki har iyayen suna kallon ta,,
dake bala'eene yahau ta da masifa,," kedin wa?dama duk
iskancin da kike tatawa a garin na samu lbr,toh dole ki
tsaida haka ki samo na aure,,ta kalle shi, "toh na tsaida,,yai
murmushi," ko ke fa,,a ina yake?ta hade rai,, "kai man,, ba
shiba hatta iyayen sai da suka zaro ido,, ya tashi," ke
banson iskancin banxa,,Tuni ta fara burburwa tana kukan
gaske,,"ni wlh kai nake so,, kuma kai zan aura,,baban ta ya
doka mata tsawa,"Sa'a bama son iskanci fa,, "ta kara jiniya"
wlh shi zan aura,, ni shi nake so,,tuni tsoho ya sau
kuka,,Lalle ya yarda BARIKI ce yan nan,, kuka yake
yana"Allah ya isa saude,,ki kalle ni kice ni zaki aura?jikar
jika ta?cikin kukan karya tace"Toh Haram ne?nidai kai za'a
abani, ba shiri yai hanyar waje yana goge kwala,
"InshaAllah anyi na karshe,,da sauri baban ya bishi," Baba
kai hakuri ka dawo,,dole ta bi umarnin ka ai,,har suka fito
kofar gida tsoho na kuka"ai ni ba ruwana da harkar yarka
daga yau,,Ashe da gaske "BARIKI ce haka??Wai ni zata
aura??Alhj Muktar suka kalli juna,tuni dariya tazo musu,,a
karshe dole baban tasha ya raka shi ya koma inda ya
fito..yana fita ta ware tana dirkar dariya.. Ladi ta fara tafa
hannu,ta nuno ta da hannu" anya Sa'a,, ta kallo Maman
tasu,"mama mey nai? Ta kar kade jikin ta,, ta sauke ajiyar
zuciya "ba komai Sa'a,, Allah ya shirya mana ke.,tace "
Amin.tai waje wajen kiran ta,,. Dariya ta samu suna dirka,
tana ganin shi ta gane shi,,tuni ta hau murmushi, "yau an
tuno Haj Ahmad? Yai murmushi" Manya a Baku naku
daban,ttai wani fari,,tuni Alhj Muktar ya gyara tsaiwa, kai
shikam BARIKI ta mishi,da aure ba contract ba.
.
Abinda ya kawo su suka sanar mata,tai murmushi, da gani
mutumin zai sau hannu, tuni ta yarda,Alhj yace da daddare
zai dawo,sai su tsadan ce,,tai murmushi, dan tuni ta harbo
jirgin shi,,kai ta kada,,sukai sallama tai gida,,Maman su ta
kalle ta, "Sa'a, ta zauna tana amsa wa,," In tambaye ki man?
tai murmushi, "toh m
Read More